✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darasin rayuwa daga labarin mai tumatir

Jama’a masu bibiyar mu a cikin wannan fili na Sinadarin Rayuwa, muna yi muku sallama; Assalamu alaikum. Bayan haka, kamar yadda aka saba, yau kuma…

Jama’a masu bibiyar mu a cikin wannan fili na Sinadarin Rayuwa, muna yi muku sallama; Assalamu alaikum. Bayan haka, kamar yadda aka saba, yau kuma mun tsinto muku wani labari ne mai dauke da kyakkyawan darasi game da rayuwa. Darussan da ke kunshe cikin wannan labari, za su yi mana matukar amfani, musamman ma matasanmu na yanzu da ke kokarin neman samun nasarar rayuwa cikin kankanen lokaci; haka kuma ba su yin wani katabus cikin kokari. Babu shakka, idan muka duba wannan labari da idon basira, za mu gane cewa lallai komai nisan tafiya, da taki daya ake fara ta. Shi kuwa gulbi, Hausawa sun ce da tsattsafi yake cika. Idan kun shirya, ga labarin:

Wani matashi ne da ya kammala karatun jami’a, kuma kwas din injiniya ya kammala, ya kuma samu kykakkyawan sakamako fiye da mafi yawan abokan karatunsa. Bayan ya kammala aikin hidimar kasa, sai ya fantsama neman aiki. Ya kwashe sama da shekara guda yana Safa da Marwa daga wannan kamfani zuwa wancan, daga wannan ma’aikata zuwa waccan, amma abin kamar an shuka dusa. Bai samu aiki ba ko daya, duk inda ya je sai a rika ce masa kodai ya sake dawowa gobe ko jibi, ko kuma a ce masa babu aikin gaba daya.

Rannan yana zaune, sai ya tuna da irin tsawon lokacin da ya bata yana neman aiki. Sai nan da nan ya shiga maganar zuci: “Yau shekara daya ke nan cur, watanni goma sha biyu ina zaryar neman aiki, amma ban samu ba.” Abin da ya fada wa kansa ke nan. “Wani abin mamaki ma shi ne, wajen kanena nake amsar kudin babur da nake hawa, wani lokacin ma har da na abinci. Ga shi kuma sana’ar tireda yake yi, wacce ya fara duka da jarin Naira dari takwas, amma yanzu yana da gidan kansa, ga shi da matar aure har ma da ’ya’ya, gami kuma da gonar da yake nomawa a kullum. Me zai hana ni ma in fara wata sana’a komai kankantarta?” 

Wannan tambaya, ita ce ta sanya shi ya canza tunani gaba daya, inda ya canza alkibla kuma ya dauki wata hanya ta daban. Hanyar da ta haifar masa da sabuwar sana’a, wacce ta tabbatar masa da cikakka kuma gamsassar nasara a rayuwa.

Abin da ya yi shi ne, ya lura da yadda kaka ta yi kyau, masu noman tumatir sun samu albarka sosai, don haka sai kawai ya je ya sawo kwando daya na tumatir. Ya shiga kasuwa da shi yana talla, inda cikin mintuna kadan ya sayar. Ya sake komawa ya sawo wani kwandon daya, shi ma ya sayar cikin lokaci. A takaice dai, daga safiya zuwa faduwar rana, sai ga mutumin naka ya sayar da kwanduna sama da goma na tumatir, kuma ya samu gagarumar riba.

Wanshekare, bai tsaya yin wata shawara ba, sai ya ci gaba da sana’ar sayar da tumatirinsa. Tun yana sayen kwando dai-dai, sai ga shi yana sayen biyu zuwa uku. Da abin ya bunkasa, sai ga shi yana tada mota cike da tumatir yana sayarwa. Sannu a hankali, tun yana kai tumatiri Kurmi yana sayarwa, sai ga shi ya zama dila, wanda kamfanoni ke saye daga hannunsa. 

Ta hanyar wannan sana’a, sai ga shi ya sayi motocin jigilar tumatur da yawa, ya samu kudi ya sayi babban filin noman rani, ya rika noma tumatir kuma yana sayen na sauran manoma. Haka kuma ta ba shi damar kafa kamfanin sarrafa tumatir na gwangwani. Cikin ’yan shekarun da ba su wuce biyar ba, duk kantunan da ka duba, sai ka ga tumatirin gwangwanin da kamfaninsa ya sarrafa. Ya zama hamshakin attajiri, sannan kuma ya samar wa dubban mutane hanyar samun abin rayuwa.

Rannan ya je masallacin Juma’a, bayan an sallame Sallah, sai wani matashi ya mike tsaye, lafiyarsa kalau, amma ya make murya, ya marairaice yana neman taimakon kudi, wai bai da sana’a, don haka bai ci komai ba tun da safe. Mutumin nan ya kira shi ya ba shi labarin yadda ya canza wa kansa rayuwa ta yin sana’a karama, wacce ta bunkasa ta zama babba. Ya dauko Naira dubu daya ya ba shi, ya ce masa ya yi amfani da ita wajen fara wata sana’a komai kankantarta.  

Jama’a masu karatu, ina fatan za a iya tsintar daya ko biyu na wasu darussa daga wanan labari na Malam Mai Tumatir. Mu dai a nan mun fahimci cewa, aikin gwamnati ba shi kadai ne hanyar samun abin duniya ba. Don haka kada mu raina sana’a komai kankantarta, don gadarar cewa mun kammala jami’a. Haka kuma, mun fahimta da cewa, girman kai babu abin da zai iya haifar mana sai talauci da kaskanci, yayin da rashin girman kai zai kai mutum ga arziki da mutunci; kamar dai yadda Mai Tumatir ya azurta da kankanuwar sana’arsa.

Lokaci ya yi da ya kamata matasanmu su gane cewa, maimakon su maida hankali wajen kallace-kallacen kwallo da fina-finai, kamata ya yi su fantsama cikin kasa domin neman arziki. Allah Bai hallicci wani rai ba, face Ya tanadar masa arzikinsa. Don haka, gara mutum ya kama sana’a ko aiki komai kankantarsa ya fi masa da ya zauna yana marairaicewa, yana yin ’yar murya ga mutane domin neman kudi. Mu jaraba mu gani, mu daina zaman banza da zaman kashe wando. 

Nan kuma za mu tsaya, sai kuma mako mai zuwa idan Allah Ya kai mu, za mu ci gaba da wani maudu’in na Sinadarin Rayuwa. Wassalam!