✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darasin rayuwa daga labarin uba da dansa (1)

Ya ku ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum! Kamar yadda muka saba, a wannan makon ma muna dauke da sabon maudu’i, wanda idan muka nazarce…

Ya ku ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum!

Kamar yadda muka saba, a wannan makon ma muna dauke da sabon maudu’i, wanda idan muka nazarce shi, zai zizara mana wani sinadari na gyara rayuwarmu, sannan mu kaurace wa wasu ’yan kura-kurai da muke yi a rayuwarmu ta yau da kullum. Irin wadannan kura-kurai da muke aikatawa, sukan jawo mana nadama a rayuwa. Kasancewar mu ba ma’asumai ba ne, ba za mu iya hana aukuwar kura-kurai gaba daya ba a rayuwarmu; amma duk da haka, za mu iya kauce wa wadanda za mu iya, musamman ta hanyar kula.

Wani labari ne dan gajere zan kawo. Na zakulo shi ne daga cikin taskokin masu bibiyar al’amuran rayuwar al’umma ta yau da kullum. Kamar yadda aka shaida mini, labarin nan ya faru a zahiri, duk da cewa ba sai mun ambaci suna ko wurin da al’amarin ya faru ba. Babban abin lura shi ne, mun fi ba labarin muhimmanci. Ke nan, ba mu damu da wurin da abin ya faru, ko sunayen wadanda abin ya shafa ba. Babban abin yi shi ne, mu kula da wani karin maganar Hausawa, da ke cewa; ‘Idan ka ga gemun dan uwanka ya kama wuta, sai ka shafa wa naka ruwa.’ Ko kuma kamar yadda suka ce, ‘Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.’

Ga yadda labarin ya kasance:

Wani magidanci ne mai mace daya da dansa daya. Yaron ya kasance dan kimanin shekara hudu da haihuwa. Yaro ne mai wayo da hazaka a makarantar da aka sanya shi ta rainon yara. Wata rana sai babansa ya samu kudi, ya canja mota. Ya sayo sabuwar mota wacce ake ya yi, kuma ya rika kula da ita kamar wutar hunturu.

Duk safiya, magidancin nan yakan goge motarsa, sannan ya dauki dan nan nasa ya kai shi makaranta, shi kuma ya wuce wajen aiki daga can. Ran nan ya fito da safe yana goge motar da tsumma, sai ga yaron ya fito, yana rataye da jakarsa ta makaranta. Ya zo kusa da baban nasa yana jingina da motar.

A kan haka da yake hannun yaro kamar hannun biri ne, sai kawai ya dauki wata ’yar kusa, ya koma can gefen motar yana kartawa. Ashe wani rubutu yake yi a jikin motar da wannan kusa da ke hannunsa. Da farko mahaifin nasa bai ankara da abin da ke faruwa ba, sai daga baya ya gani.

Me zai faru? Mutumin nan sai kaunar motar nan ta makantar da shi, ya harzuka matuka. Ya mance da kaunar da yake wa yaron nan, ya mance cewa dukiya mai karewa ce. Bai san lokacin da ya dauki wata wayar kebur ba, ya bazama da gudu zuwa inda yaron nan yake. Ya yi ta shauda wa yaron nan kebur a hannuwansa. Jini ya kece daga yatsunsa, dukkan yatsun suka samu mugun rauni.

Za mu ci gaba