✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darren Fletcher zai zama Daraktan wasanni a kulob din Man United

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Manchester United na Ingila sun nuna kulob din ya fara tantance  mutanen da suka nuna sha’awarsu ta zama…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Manchester United na Ingila sun nuna kulob din ya fara tantance  mutanen da suka nuna sha’awarsu ta zama daraktan wasanni a kulob din.

Rahoton ya nuna tsohon dan kwallon kulob din Man Uniteds Darren Fletcher ne yake sahun farko a jerin wadanda ke neman a ba su wannan mukami kuma ga dukkan alamu kulob din zai ba shi damar rike wannan matsayi nan ba da jimawa ba.

Kulob din ya ce zai dauki daraktan wasanni ne wanda zai rika taimakon kocin kulob din Ole Gunnar Solskjaer a kaka mai zuwa.

Dareen Fletcher ya buga wa Manchester United kwallo fiye da sau 300 kuma ya bar kulob din ne a watan Janairun 2015 inda ya koma na West Brom da ke wasa a rukunin ’yan dagaji.  A yanzu dan kwallon ya shiga sahun masu neman mukamin Daraktan wasanni ne a kulob din United don bayar da tasa gudunmawa wajen farfado da martabar kulob din a idon duniya kuma alamu sun nuna mahukunta kulob din suna tunanin ba Fletcher damar rike wannan matsayi a matsayinsa na tsohon dan kwallo a kulob din.