daruruwan magoya bayan PDP sun koma APC a yankin Lere

A ci gaba da dambarwar siyasar da ke faruwa a kasar nan, daruruwan magoya bayan Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna sun canja sheka zuwa Jam’iyyar APC a karshen makon jiya.
Da yake jawabi a wurin taron da Jam’iyyar APC ta shirya a garin Saminaka don karbar ’ya’yan PDP din, jagoran wadanda suka canza shekar kuma shugaban Jam’iyyar PDP na mazabar dan Alhaji, Alhaji Abdulrazak Yahaya ya ce su magoya bayan Jam’iyyar PDP da suka koma Jam’iyyar APC a mazabu 11 na karamar hukumar sun kai 2,301.
Ya ce “Babban burinmu na wannan canjin sheka zuwa APC, shi ne mu ga cewa a samu canji a Jihar Kaduna da Najeriya baki daya. Domin PDP ba ta kawo komai na alheri ba a jihar da Najeriya.” Ya ce wannan wata guguwar wargajewa ce ta taso wa Jam’iyyar PDP a Najeriya.
Wani jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Balarabe Ibrahim ya ce PDP ta zo da kabilanci da rashin tsaro da rashin ilimi da rashin kiwon lafiya, amma duk da haka mutanen jam’iyyar suna son su zarce.
A jawabin wanda ya karbi masu canja shekar, kuma dan kwamitin hadaka na Jam’iyyar APC a Shiyyar Kaduna ta Arewa Malam Yunusa Manu Saminaka ya ce babu shakka zuwan wadannan mutane Jam’iyyar APC a karamar Hukumar Lere alheri ne mai yawa.
Ya yi kira ga sauran magoya bayan Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Lere su dawo Jam’iyyar APC domin samun mafita, domin kowa ya san PDP a karamar hukumar a wargaje take. Ya ce talakawan kasar nan, sun san babu wani alheri da ke tattare da mulkin PDP, don haka kowa ya yi kokari ya dawo APC domin samun adalci.

Share