✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (10)

A makonn jiya, mun ji yadda Malam Baba ya gamsar da Baban Larai, inda ya bayyana masa shawara ta biyu daga cikin shawarwari uku da ya…

A makonn jiya, mun ji yadda Malam Baba ya gamsar da Baban Larai, inda ya bayyana masa shawara ta biyu daga cikin shawarwari uku da ya yi alkawarin ba shi. A wannan makon kuma za mu ji shawara ta uku da zai ba shi. Sai a biyo domin jin yadda za ta kaya.

“Tunda na ga ka fahimci abubuwa biyu da na bayyana maka, bari kuma yanzu ba tare da bata lokaci ba in gaya maka cikon na ukun.” Abin da Malam Baba ya fada wa Baban Larai ke nan, lokacin da ya ga hankalinsa ya kara kwanciya.

“A kullum, ka rika tuna wannan: ‘Kada ka yi fushi!’ Fushi na daya daga cikin munanan al’amura da ke hallaka mutane, yake jaza musu asara da takaici a mafi yawan lokaci.” Malam Baba zai ci gaba da bayani sai ya ga kamar Baban Larai ya canja fuska cikin mamaki, har ma ya yunkura zai yi magana, amma sai ya dakatar da shi da hannu, ya ci gaba da bayaninsa.

“Na san abin zai ba ka mamaki, a ce wai mutum kada ya yi fushi. To lallai dai haka al’amarin yake. Duk wani mataki da za ka iya dauka a rayuwarka domin ya hana ka yin fushi, to ka yi kokarin daukarsa. Abu ne mai wahalar gaske a ce mutum zai daina yin fushi a rayuwarsa, amma idan ka saurare ni cikin natsuwa da fahimta, za ka ga cewa hakan mai saukin aiwatarwa ne.”

Baban Larai ya sake natsuwa don ya ji yadda mutum zai magance matsalar fushi.

“Idan na ce kada ka yi fushi, ba ina nufin cewa ba za ka yi fushi ba ne kwata-kwata a rayuwarka, babban abin da ake nufi shi ne, kada ka sake ka dauki wani mataki ko ka zartar da hukunci alhali kana cikin fushi. Babu shakka duk wani dan Adam, akwai abin da zai iya bata masa rai ko  ya harzuka shi. Idan haka ya faru, me ya kamata ka yi? Shi ne na ce maka ‘Kada ka yi fushi.’

“Me ya sanya fushi ya kasance abu mai muni, kuma marar alfanu ga mutum?” Tambayar da Malam Baba ya yi wa Baban Larai ke nan, amma bai jira ya ba shi amsa ba sai ya ci gaba da bayaninsa.

“Fushi dai, kamar yadda ingantattun bayanai suka gabata, daya daga cikin makamai ne na Shaidan. Haka kuma, daya daga cikin alburusan wuta ne. Idan mutum ya yi fushi, komai zai iya aikatawa, wanda kuma duk wani abu da za a aikata, idan dai a cikin fushi ne, to ba mai kyau ba ne. Duk wanda ya lizimci yanke hukunci ko aiwatar da wani abu, alhali yana cikin fushi, to zai yi nadama daga baya, domin kuwa babu alheri ga duk abin da aka aiwatar a cikin fushi.”

 

Za mu ci gaba