✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (4)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari…

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:

“Ita wannan mata, ta samu kanta ne cikin wata irin rayuwa mai wuyar sha’ani.” Malam Baba ya ci gaba da bayaninsa. “Ta kasance matar aure, wadda ke auren wani attajiri. Sun yi aure ne tun bai mallaki dukiyar da yake da ita ba yanzu. Suna son juna kwarai matuka, matsalolinsa nata ne, haka ita ma nata nasa ne. Yau da gobe suna zaman fahimtar juna, sannu a hankali sai matar ta fara shiga wasu sha’anoni na daban, wadanda a da can baya ba ta yin su. Ta kasance tana tare da wadansu karkatattun kawaye, wadanda suke kawo mata tsegunguma. Yau sai su kawo mata zancen uwar miji, ko kuma su kawo mata zancen ’yan uwansa ko abokansa. Ita kuma sai ta dauka ta sanya a zuciyarta. Ana kan haka sai ga shi dabi’unta sun canja. Mijinta ya rasa kanta ya rasa gindinta, al’amarin da ya sanya shi shiga damuwa mai yawa.

Ya ci gaba da bayaninsa, yana cewa: “Ana kan haka kuma sai dukiyarsa ta fara habaka, sannu a hankali dai ya zama attajiri sosai. Bisa kan haka ya kara aure, ya kasance mai mata biyu. Wannan aure da ya kara, shi ya kara saka rayuwar matarsa ta farko cikin garari. Abubuwan sai suka taru suka cakude mata. Miyagun kawayen nan da take tare da su, suka kara ingiza ta cikin bala’i, domin kuwa baya ga tsegunguman da suke kai mata, sai ma wadansu daga cikinsu suka hada ta da bokaye; wai domin ta samu nasarar mallake mijinta, sannan  ta samu galaba kan kishiyarta.

“Bisa ga haka sai zama tsakaninsu ya munana, a dole mijin nan nasu ya raba musu gida, kowace da nata gidan. Maimakon al’amari ya yi wa uwargidan sauki, sai ya kara bunkasa. Ta zama kamar mai rariyar hannu, duk abin da ta samu sai ya lalace. Wannan al’amari ya sanya ta fara ganin bakin kowa. Ta shiga rigima da fada da kowa. Tun daga kan mijinta da makwabtanta da sauran abokan zaman da Allah Ya hada ta da su, ba ta daraja kowa. A kullum tunaninta yana ba ta cewa ba su kaunarta.

“In gajarce maka labari, wannan mata dai ta zama wata annoba cikin unguwarsu. Ita kanta ba ta da sukuni, domin kuwa tana cikin tunani da damuwa. Duk wani abu da Allah Ya ba ta, sai ta raina, gani take kishiyarta ta fi ta komai, sannan mijinta, tana ganinsa kamar abokin gabanta. Ko ya kwantar da hankali ya yi mata bayani, ba ta saurarensa, domin kuwa bai ma ishe ta ba. Wannan dalili ne ya sanya ya yi watsi da ita. Tsakaninsa da ita, sai dai ya aika mata da kayan abinci da kudin cefane, domin kuwa gidanta ma bai shigo a gare shi. Kafin ya dauki wannan mataki, kullum ya shiga gidan, babu wata maganar alheri da ke fitowa daga bakinta a kansa. Haka kuma, idan ya kalli yanayinta da al’amarin da take ciki, sai hankalinsa ya rika tashi.

“Mijinta, domin ya samo kanta, ya dauki matakai masu yawa amma a banza. Ya aika gidansu, an zo an yi mata nasihohi, ta dan saduda. Kamar ta gyaru, bayan kwana biyu sai ga shi ta koma ’yar gidan jiya. Akwai makarantar Islamiyya da take zuwa, mijin ya samu malaminsu ya shaida masa abin da ke gudana. Bayan ta saurari hudubarsa, amma duk a banza, kamar an shuka dusa. Dalili ke nan suka tara ta gefe daya, suka zuba mata ido, sai dai addu’a.

Za a ci gaba