Search
Subscribe
Darussan rayuwa daga nasihar dattijo (2)

Darussan rayuwa daga nasihar dattijo (2)

Ya ku ma’abuta bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, yau za mu ci gaba da gudunmawar labarin LAWAL MU’AZU BAUCHI, wanda ya bijiro mana da darussa masu kyau game da rayuwar nan tamu ta duniya. Ga yadda karashen labarin ya kasance, sai mu nazarce shi cikin tsanaki:

Yayin da na kai shekara 40 kuwa, na samu kwangila ta miliyoyin kudi, sai ga sunana ta ko’ina a labarai. ’Yan uwa da abokan arziki suka yi ta tururuwa zuwa gidana, kowa da irin tasa matsalar. Cikin mako guda kuwa duk na kashe musu kudin. Wadansu sun karbi bashi da niyyar za su biya ni amma ina, suka ki biyana don na samu in karasa kwangilar da aka ba ni. Sakamakon haka aka tura ni gidan kaso, na tsawon shekara shida.

“Ina fitowa kuwa, bayan na gama shekara shida, mutane duk suka yi min watsewar zabi. Kuskuren da na yi guda daya ne a duk tsawon lokacin nan kuma yanzu na fahimci gaskiya. Bari in fada maka kuskurena – na ki na saurari kaina, na watsar da duk kyawawan tunanina; na biye wa wadansu. Yanzu ai ka ga ni kadai na zo asibitin nan, ba ’yan uwa suka kawo ni ba saboda ba ni da komai kuma ba ni da kowa. Allah Shi ne gatana, ni ne kuma gatan kaina.

“Ka ga a wannan zamanin, yana da matukar kyau ka saurari kanka, ka yi nazari mai kyau, ka yi fada ga kanka, ba sai ka jira wadansu sun tsara maka rayuwarka ba. Aka ce yana da kyau ka nemi shawara wajen mutane amma kin sauraren kanka shi kuma ya fi hadari.

“Idan ka je gida yanzu, ka zauna, ka nemi ruwa mai sanyi ka sha. Idan ka rufe idanuwanka ko kuma ka bar su a bude, duk dai yadda ka yi. Ka yi magana da kanka, ka saurari abin da ka ce wa kanka.

“Za ka iya ka dauki hanyar unguwarku kai kadai, kana tafiya kana nazarin rayuwa, ka ji abin da zuciyarka za ta fada maka. Duk duniya, Ubangiji ne kawai zai zama ma’abucin rayuwarka, wanda Shi ne zai tsara maka komai a rayuwa. Ka ga Shi ne kawai Ya cancanta ka bi abin da Ya tsara maka a rayuwarka, ko ka saurare Shi, amma bayan Shi, kada ka biye wa dan Adam. Ka zama mai sauraren abin da ka yi nazari ga kanka.

“Na san yanzu duk abubuwan da na fada maka, ba lallai ba ne su yi maka amfani amma dai ka zama mai ra’ayin kanka. Kada ka biye wa mutanen duniyar nan.”

Wannan ita ce huduba kuma nasihar dattijo. Shin ko za mu saurare shi, ko za mu dauki darasi daga rayuwarsa? Allah Ya sa mu dace, amin.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin