✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 60: Daular Larabawa ta taya Najeriya murna

Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi murnar cikar Najeriya shekara 60 sa samun ‘yancin kai. Kasar ta yi wa shahararren katafaren ginin Burj Khalifa zayyana…

Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi murnar cikar Najeriya shekara 60 sa samun ‘yancin kai.

Kasar ta yi wa shahararren katafaren ginin Burj Khalifa zayyana da ruwan tutar Najeriya a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2020, domin taya Najeriya murna.

Burj Khalifa da ke birnin Dubia na kasar UAE, na da tsawon kafa 2,722 da hawa 163, kuma shi ne bene mafi tsawo a duniya.

Jakadan UAE a Najeriya Fahad Al Taffaq ya ce kasarsa ta yi hakan ne domin yaba kyakkyawan alaka da ke tsakaninta da Najeriya da kuma nuna sanin darajar ‘yan Najeriya.

Ya yi wa Najeriya fatan alheri tare da bayar da tabbacin goyon bayan kasarsa wajen gabin Najeriya ta samu karin cigaba a nan gaba.