✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daure wa karya gindi

A ’yan kwanakin nan ne aka yi ta yada labarin wata yarinya ’yar kabilar Gbagyi (Gwari) daga Jihar Neja da aka ce Jami’ar Ahmadu Bello ta…

A ’yan kwanakin nan ne aka yi ta yada labarin wata yarinya ’yar kabilar Gbagyi (Gwari) daga Jihar Neja da aka ce Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta ki daukarta ta karanta fannin likita saboda wai ita Kirista ce, duk da cewa ta samu kyakkyawan sakamako a jarrabawarta.

Kamar yadda aka bayyana, ita wannan yarinya mai suna Goodness Thomas ’yar shekara 16 ta samu maki 302 a jarrabawar shiga jami’a ta Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Kwalejoji (JAMB) kuma tana da sakamako mai kyau a jarrabawarta ta sakandare, saboda haka ta nemi Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta dauke ta domin ta yi karatun fannin likita amma wai sai jami’ar ta ki daukarta saboda ita Kirista ce, kamar yadda kafofin watsa labarai na sada zumunta suka yi ta yadawa.

Wannan ya sanya Hukumar Jami’ar Igbinedion da ke Okada a Jihar Edo ta yanke shawarar daukar yarinyar domin ta yi karatun likita a jami’ar tare da tallafin karatu cikakke. Ta yi haka ne domin share wa yarinyar hawaye daga wariyar da aka ce wai Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta nuna mata saboda addininta.

Sai dai kuma bayanan da suka fito daga Jami’ar Ahmadu Bello sun nuna cewa ba an ki daukar yarinyar ba ce, an ba ta fannin Nazarin Bangarorin Jiki ne (Anatomy) maimakon Fannin Nazarin Fida da ta nema (Surgery and Medicine). Saboda haka sai wadansu suka yi tsalle suka yi ta watsa labaran cewa an ki daukarta a jami’ar ce saboda ita Kirista ce.

Ita kuma Jami’ar Igbinedion ba tare da binciken lamarin ba, sai ta fusata ta dauke ta tare da ba ta fannin da take so ta karanta har da ba ta tallafin karatu cikakke domin ta kunyata Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da ake zargin wai tana nuna wa mabiya addinin Kirista wariya.

Su kansu wadanda suka rika yada labarin babu wanda ya ce ya tuntubi Jami’ar Ahmadu Bello domin jin ko gaskiya ta yi wa wannan yarinyar wannan cin zarafi ko kuwa karya ce,  idan kuma gaskiya ce me ya sanya ta yi haka?

Babban abin takaici shi ne yadda Jami’ar Igbibedion ta yi saurin daukar mataki ba tare da bincike ba, duk kuwa da cewa tana iya tuntubar Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta ji dalilinta na yin haka, tunda ita ma jami’a ce da shugabanninta suke da alaka da sauran shugabannin jami’’o’in kasar nan. Amma Hukumar Jami’ar Igbinedion ba ta yi haka ba, sai ta fusata ta daure wa karya gindi.

Babu yadda za a yi a ce Jami’ar Ahmadu Bello ta ki daukar daliba wai saboda ita Kirista ce, hankali ba zai dauka ba, domin ba yau ne jami’ar ta fara daukar dalibai domin yin karatu a fannin likita ba, hasali ma ita ce jami’a ta farko a yankin Arewa da ta fara koyar da wannan fanni, kuma akwai malamai Kiristoci da dama da ke koyarwa a wannan fanni na jami’ar, ta yaya za a rika daukar malamai Kiristoci domin su koyar da aikin likita amma a ki daukar dalibai Kirista? Duk mai hankali ya san haka ba zai taba yiwuwa ba.

Shi kansa Shugaban Hukumar Jarrabawar Shiga Jami’o’i (JAMB), Farfesa Ishak Oloyede cewa ya yi wannan yarinyar ba ta samu adadin makin da za ta karanta fannin fida a Jami’ar ABU ba, jami’ar ma ta kyautata mata ne da ta dauke ta, ta ba ta fannin Nazarin Bangarorin Jiki (Anatomy) .

Wata majiya a Jami’ar ta ABU ta bayyana cewa dalibai dubbai ne suka nemi gurbin karatun likita a Jami’ar ta ABU a wannan shekarar kuma mutum 200 ne kacal za a dauka, sannan akwai dalibai da yawa da suka samu makin da ya fi na Goodness Thomas, ga kuma wadanda manyan kasa ke turo su domin a dauke su.

Ya kamata wannan abu da ya faru ya kara zama darasi ga mutanen kasar nan wajen ganin suna tantance sahihancin labari kafin su dauki mataki a kai. Bai kamata a ce mutane masu hankali da ilimi kamar mahukunta Jami’ar Igbibedion sun yi amfani da labarin karya wajen gudanar da harkokinsu ba.

Yanzu dai an cusa wa wannan yarinya Goodness Thomas ’yar shekara 16 kyamar addinin Musulunci, ga shi kuma likita take son ta zama, zai wuya idan za ta ga marasa lafiya Musulmi ya kasance ba ta rika jin wani abu a zuciyarta ba. Allah Ya sawwake.