✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daurin auren ’yar Mu’azu ya hada jiga-jigan APC da PDP a Bauchi

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya bayyana a Bauchi domin aurar da ’yarsa, inda jiga-jigan…

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya bayyana a Bauchi domin aurar da ’yarsa, inda jiga-jigan ’yan siyasa suka hallara.

Alhaji Ahmadu Mu’azu dai ya shafe sama da shekara uku baya cikin kasar nan, inda ya fice waje jim kadan da gudanar da  babban zaben shekarar  2015.

Wani makusacin tsohon Gwamnan ya ce Alhaji Ahmadu Mu’azu ya iso Abuja ne daga kasar wajen ranar Juma’a ya kuma zarce zuwa Bauchi don halartar auren ’yar tasa wacce aka daura a fadar Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu.

Wannan aure ya hado jiga-jigan ’yan siyasa kuma kusoshi daga jam’iyyun APC da PDP duk da bambancin siyasa da ke tsakaninsu.

Cikin wadanda suka halarta akwai Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar da Shugaban PDP na Kasa, Uche Secondus da gwamnonin jihohin Gombe da Bauchi, Ibrahim Hassan Dankwambo da Mohammed Abdullahi Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda da manyan ’yan siyasa da malamai da sarakuna daga ciki da wajen jihar.

Da yake daura auren, Babban Limamin Bauchi, Alhaji Bala Ahmad Baban’inna ya bayyana sadakin auren a kan Naira dubu 100  sannan ya roka wa ma’auratan, Mohammed Sagiru Haruna Suleiman da amaryarsa Sai’datu Ahmadu Mu’azu zama lafiya da kwanciyar hankali da kuma zuriya dayyiba.

Kamar yadda suka saba, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Mahmud Yayale Ahmad ne ke ba da auren ’ya’yan Ahmadu Mu’azu a wannan karon ma shi ya ba da auren yayin da Alhaji Magaji Turakin Gwandu ya karbi auren a madadin ango.