Daily Trust Aminiya - Dele Momodu ya barke da kuka kan Abiola
Subscribe

Dele Momodu ya barke da kuka kan Abiola

A makon jiya ne sanannen mawallafin mujallar attajirai  ‘yan kwalisa ta ‘Obation’ kuma mai tallafa wa mawaka da ’yan fim a Kudancin Najeriya, Dele Momodu ya ba mutane mamaki, inda aka ga ya barke da kuka da hawaye share-share, musamman domin nuna alhininsa ga marigayi Chif M.K.O. Abiola.
Kamar yadda Aminiya ta kalato, Dele ya tuna da marigayi Abiola ne, a sakamakon jawabin ’yarsa da ya ji a tashar talabijin ta BBC, wadda ta bayyana cewa mahaifin nata ya sha dauri a kasso, ya mutu a can a lokacin da take ’yar shekara 12 a duniya.
Dele Momodu, a yayin da yake hawaye, cike da alhinin tunowa da Abiola, fitaccen dan siyasar da ya mutu a 1998, ya ce: “Wannan mata, Dupe Abiola, ta yi jawabi mai ratsa zukata game da babanta, wanda ya sha dauri a lokacin tana ’yar shekara 12 a duniya, sannan ta fadi yadda ya rasa ransa a kasso, lokacin da take da shekara 16.”

texem
More Stories