Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Diego Costa zai koma Ingila

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun ce tsohon dan kwallon Chelsea da yanzu haka yake wasa a Atletico Madrid, Diego Costa ya fara yunkurin sake komawa Ingila don ci gaba da kwallo. Sai dai a wannan karo yana yunkurin komawa kulob din Wolberhampton ne.

Costa ya yi wasa a Chelsea  a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017 inda ya lashe Kofin Firimiya sau biyu da Kofin Kalubale (FA) sau daya daga nan ne ya sake komawa asalin kulob dinsa Atletico Madrid na Sifen.

ADVERTISEMENT

Sai dai ganin yadda yake yawan samun sabani  da Koci Diego Simeone na Madrid ya sa ya yanke shawarar canja sheka zuwa Wolbes a bana.

Costa mai shekara 30 ya buga wa kasar haihuwarsa Sifen wasanni da dama.

ADVERTISEMENT