✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dillalai sun koka kan rufe kamfanonin Koka-Kola a Arewa

Dillalai masu harkar lemon kwalba na Kamfanin NBC mai yin Koka-Kola da sauransu sun koka kan asarar da suke tafkawa sakamakon rufe rassan kamfanin a…

Dillalai masu harkar lemon kwalba na Kamfanin NBC mai yin Koka-Kola da sauransu sun koka kan asarar da suke tafkawa sakamakon rufe rassan kamfanin a Arewacin kasar nan da kamfanin ya yi. Dillalan sun kuma koka kan yadda kamfanin yake rarraba musu kaya, inda suka ce tun bayan rufe wasu daga cikin rassansa na Arewa suka shiga cikin tsaka- mai-wuya domin ba sa iya biya wa  abokan hulda bukata kamar lokacin da kamfanin yake gudanar da aikinsa a Arewa. Kamfanin shi ke samar da lemon kwalba na Koka-Kola da Fanta da kuma Sprite.

A wani bayani da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Intanet ya ce kamfanin yana da rassa 11 amma tara 9 daga ciki ne kawai suke aiki wadanda suka hada da wanda ke Babban Birnin Tarayya, Abuja da kuma jihohin Oyo da Edo da Kano da Enugu da Legas da Borno da Imo da kuma Ribas.

Kamfanin ya rufe rassansa na jihohin Filato Kaduna. Kuma ya so rufe na Kano kafin wani basarake ya sa baki a dakatar.Kawo yanzu dai kamfanin yana da rassa 3 ne kawai a jihohin Arewa 19 .

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa manyan dillalan kamfanin da ke Jihar Kaduna sun koka kan asarar da suke yi domin suna kama hayar manyan sito-siton ajjye kaya na miliyoyin Naira amma saboda rashin aikin da kamfanin ke yi a jihar ya sa ba sa samun kayan da ya kamata su sayar domin su ci ribar da za su iya biyan kudin hayar da suka karba.

Dillalan suna samun kashi 30 cikin  100 ne kawai na kayan da suke karba kafin a rufe kamfanin a jihar, wannan ya haifar wa dillalan matsala domin sun kama hayar wuraren ajiyar kaya kuma a irin wannan lokaci ne suke maida asarar rashin cinikin da suke yi a lokacin sanyi.

A garin Jos kuwa dillalan cewa suka yi tun bayan rufe kamfanin sai dai a shigo musu da kaya daga Ibadan a Jihar Oyo. Dillalan suka ce bayan rufe kamfanin wanda ke kan Titin Yakubu Gowon an mayar da shi zuwa wajen ajiye kaya na kamfanin.

Wani dillali ya ce “Abin takaicin shi ne yadda abokan hulda suke zuwa daga kasar Nijar domin neman lemon Koka -Kola. Ba mu san me ke faruwa a Kano ba domin da akwai wadatar kayan a can to da ba za ka ga baki suna kokawa ba kan rashin kayan.”

“Rufe reshen kamfanin da ke nan Jos ba karamar illa ya yi mana ba kuma ga shi mutane sun rasa ayyukansu. Kamfanin yana so ne ya rage kashe kudi wajen sarrafa kaya sannan ya ninka ribar da yake samu,” inji shi.

“Abin takaici shi ne an rufe kamfanin a nan Jos. Mutane sun rasa ayyukan yi sannan an kara samar da wasu guraben aiki a Ibadan da Legas domin dole ne kamfanonin da suke can su kara daukar ma’aikata domin su samar da kayan da ake nema a nan Jos da sauran jihohin Arewa don haka sun kassara mu sun dauke aikin yi daga nan sun mai da shi jihohin Kudu maso Yamma.

A lokacin da yake zantawa da Aminiya Darakatan Sadarwa na Kamfanin NBC, Mista Ekuma Eze, ya tabbatar da rufe wasu rassan kamfanin. Ya ce wannan ya faru ne saboda su rage yawan kudaden da kamfanin yake kashewa wajen sarrafa kaya.

Ya ce ba gaskiya ba ce cewa wani basarake wai ya sa baki wajen rufe wani reshensu ba.

“Mun kara fadada reshenmu na Kano da Legas da Imo da Fatakwal. Ragowar rassan da muka rufe mun mayar da su wajen a jiye kaya da rarraba su, kamfani daya yana sarrafa kayan da wasu rassa biyar suke sarrafawa don haka babu yadda za mu ci gaba da kashe kudade,” inji shi.