✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dilolin kayan gini a Sakkwato sun yaba da Kamfanonin Royal Exclusive da WACL

Dilolin kayan gini a Jihar Sakkwato sun yaba da Kamfanin kayan gini na West African Ceramics Ltd da ROYAL brand bisa fito da tsarin katafaren…

Dilolin kayan gini a Jihar Sakkwato sun yaba da Kamfanin kayan gini na West African Ceramics Ltd da ROYAL brand bisa fito da tsarin katafaren shagon kaya na Royal Exclusive Showroom a jihar.

Sun bayyana jin dadinsu ne a lokacin da ake kaddamar da sabon dakin ko shagon na nuna kayayyakin gini a layin Sheikh Abdulrahman Sudais da ke Sakkwato.

Kakakin WACL, Emmanuel Udoro ne ya bayyana hakan a wata takardar, inda ya ce hadakar an yi shi ne domin karfafa gwamnati wajen habaka bangaren da kuma bunkasa kayayyakin cikin gida.

“Wannan tsarin zai taimaka wajen samar wa magina da masu ginin da sauran masu da tsaki a harkokin gini wajen rage asara da kuma samun saukin da kuma samun kaya cikin sauki,” inji shi.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar dad akin kayayyakin, Manajan Darakta, Ribalka Nig. Ltd Alhaji Ribado Aliyu ya ce wannan tsarin shi ne na farko a Jihar Sakkwato, wanda kuma a cewarsa zai kawo sauki ga dilolon kayan gini a Sakkwato da makwabtansu na Kebbi da Gusau.

“Ina matukar farin ciki samun wannan sabon tsarin na samar da babban shagon kayayyakin gini na Royal Exclusive a Sakkwato saboda dalilai da yawa. Na farko, shi ne irinsa na farko a Sakkwato. Na biyu kuma an taimaka wa diloli da abokanan hulda wajen samar da kaya mai sauki da rage asara, domin yanzu ba sai mun yi tafiya mai nisa ba zuwa Kano ko Kaduna wajen samun wadannan kayayyaki.

“Yanzu duk wadannan abubuwan da ake bukata mun samar da su cikin sauki. Mu muka samar da babban dakin ajiyan ko shago, sai WACL suka samar da kayayyakin.”

Shi ma a nasa jawabin, Manajan Tsare-tsare na WACL, Alhaji Abdulrahim Bello, wanda ya samu wakilcin Janar Manaja, Mista Bhaskar Rao cewa ya yi, “hadakar na tsakanin Ribalka Nig Ltd mun yi ne saboda burin da muke da shi na tabbatar da cewa mun tallafa wa bangaren gine-gine da samar da gideje masu sauki a Najeriya kuma masu karko da inganci da rahusa.”

Bello ya kara da cewa katafaren shagon kayayyakin zai taimaka wajen wayar da kan magina wajen sanin kayan gini masu inganci.