✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dinkunan Sallah: Hattara ’yan mata

Daga Maccido Isah da Nasir AbbasDa sunan Allah mai rahama mai jinkai.Ganin lokacin bikin sallah ya karato, kuma ‘yan mata sai rububin bayar da miyagun…

Daga Maccido Isah da Nasir Abbas
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.
Ganin lokacin bikin sallah ya karato, kuma ‘yan mata sai rububin bayar da miyagun dinkuna suke, to su sani wadannan dinkunan su ne za su lalata dukkan lada da tarbiya da suka samu a watan da zai shude (Ramadana), hakan ne ya sa muka ga dacewar yin tsokaci don mu ja hankalinsu.
Bari mu fara da tunatar da ku wani hadisi- an karbo daga Abdullahi dan Umar Allah Ya yarda da shi, manzon Allah (SAW) ya ce: “Da sannu wasu mazaje za su zo a karshen wannan al’ummar, wadanda ke hawan wasu ababen hawa masu sirduna da taushi, har su zo kofofin masallantansu, matansu sanye suke da tufafi amma kuma a tsirara suke. Kawunansu kai ka ce tozon rakumi ne! Ku la’ane su hakika su la’anannu ne….”
A cikin wannan hadisin da ke sama, muna iya fahimtar cewa sanya tufafi ba shi ne rufe al’aura ba, har sai mace ta sanya tufafin  da shari’a ta tanadar, domin abin da ake nufi da fitar tsiraici shi ne, mace ta sanya suturar da ba za ta rufe mata gabban da shari’a ta umurce ta ta rufe su ba. Ke nan tufafin da ‘yan matanmu ke sanyawa masu sunaye daban-daban kamar: nuna min bayanki da sa hannunka masoyi da sauransu ba tufafi ba ne a shari’a. Kuma wadda take sanye da su tsirara take. Haka ma akwai maganar karin gashin kai da wasunsu ke yi abin da muka fi sani da ‘A CUCI MAZA! Tsarki ya tabbata ga Allah! Abin da ya fi ban tsoro a cikin lamarinsu shi ne, manzo Allah (SAW) ya yi horo karara da mu la’ane su domin su la’anannu ne.
Da wannan muke ba ku shawara idan kuna da niyyar irin wannan shigar kada ma ku soma, domin babu ko shakka hakan zai jawo muku la’ana, kuma za mu la’ane ku tun da manzon Allah (SAW) ya la’ani wadanda suka yi shigar tsiraici kuma ya ba da damar a la’ane su.
Albishirinku mata? Wallahi da kun yi irin wannan shigar, kuma kuka ga wani ya daga kai ya yi muku kallon kirki  ko ya nemi yaba ku, to ku sani shi ma ya shiga cikin la’ana.
Hakika mata kuna neman zamewa fitina da tashin hankali ga wannan al’ummar ta hanyar wannan shigar tsiraici da kuke yi, kamar yadda ya tabbata cewa Manzon Allah SAW ya ce, “ban bar wata fitina a bayana mafi cutarwa ga mazaje ba kamar mata. Don haka wannan shigar ce take rikirkitarwa tare da dagula al’amura musamman a ranakun bikin sallah, sai mata la’anannu su yi ta jan hankalin mazaje, abin da yake kai wa zuwa ga sabon Allah a wannan rana mai daraja.
Haka kuma sanannen abu ne cewa mafi girman abin da kowace mace za ta mallaka kafin ta samu kamala da daukaka su ne, kunya da kamewa, kuma kiyaye wadannan siffofin su ne kariyar mutuncin kowace `ya mace da kuma cikar kamalarta, bai kamata sai mace mai hankali ta yi jifa da kamalarta, kunyarta da kuma kamewarta, ta rika yin fita ta tsiraici ba, domin  fitar tsiraici ba abin da ke haifarwa illa kaskanci da tozarci ga duk mai yin ta har da ma al’ummar da ake yin fitar tsiraici a cikinta. Shin hakan bai ishe ku kunya ba, a ce abin da ya kamata ku killace shi daga ganin kowa face wani mutum daya tak da Allah ya halatta muku, sai ku dawo kuna tallarsa a kan titi a banza! Kash! Amma wasu mata na abin kunya da sunan wayewa. Mece ce daraja a cikin abin da aka bayyana kowa na kallo a kan hanya? Karuwanci ne ko da ba a kira shi da sunan ba.
Shaidan fa yana amfani da mata wurin yin galaba a kan mazaje, ko da kuwa matan masu kamewa ne ta hanyar yin shigar kirki, to ballantana masu yin fitar tsiraici. Kamar yadda Annabi (SAW) ya fada a cikin wani hadisi cewa;- “mace tana fuskantowa ne a cikin surar shaidan, kuma tana bayar da baya ne a cikin surar shaidan.”
Ya ku bayin Allah! Ku sani fa aljanna tana jiranku kamar yadda wutar jahannama ke jiranku, zabin kuma ya rage naku. Manzon Allah SAW yana cewa “Dukkan al’ummata za su shiga aljanna sai fa wanda ya ki’’ Sai sahabbai suka tambaye shi “Wa zai ki ya manzon Allah?’’ Sai ya ce da su: “Wanda ya yi min da’a zai shiga aljanna, wanda kuma ya saba min,shi ne ya ki.’’ Don haka yin fitar tsiraici saba wa manzon Allah ne, kuma saba masa, guje wa aljanna ne zuwa wuta.
Haka ma fa daga cikin yarjejeniyar da Manzon Allah (SAW) yakan yi da matan da ke zuwa domin su musulunta, akwai sharadin ba za su yi fitar tsiraici ba kamar yadda Imamu Ahmad ya ruwaito, a lokacin da Umaimatu ta zo domin mika mubaya’arta gare shi. Wannan kuma duk yana nuna mana hadarin da ke cikin aikata shigar tsiraici ne. Akwai hadisi sananne da ke nuna cewa: mai shigar tsiraici, ba za ta ma ji kamshin aljanna ba ballantan ma ta shige ta.
Ya Allah muna rokon Ka shiryar da mu kan tafarki madaidaici.
Daga Maccido Isah Siriddawa da Nasir Abbas Babi
08032818024
08033186727