Search
Subscribe
Dino Melaye ya kama hanyar adabo da Majalisa

Dino Melaye ya kama hanyar adabo da Majalisa

Smart Adeyemi, na jam’iyyar APC, wanda shi ne abokin takarar Sanata Dino Melaye, na jam’iyyar PDP, a zaben kujerar Majalisar Dattawa na yankin Kogi ta Yamma ya kama hanyar lashe zaben da aka yi jiya – inda suka fafata a zaben.

Sakamakon zaben Kanana Hukumomi 6 cikin 7 na mazabar sun bayyana, kamar yadda hukumar zaben ta kasa, INEC ta sanar.

Ga yadda INEC ta sanar da sakamakon kamar haka:

Sakamakon Karamar Hukumar Ijumu

APC – 11,425

PDP – 7,587

Sakamakon Karamar Hukumar Kabba/Bunu

APC – 15,037

PDP – 8,974

Sakamakon Karamar Hukumar Yagba ta Gabas

APC – 6,633

PDP – 7,745

Sakamakon Karamar Hukumar Mopa/Muro

APC – 4,874

PDP – 3,704

Sakamakon Karamar Hukumar Yagba ta Yamma *

APC – 7,868

PDP – 8,860

Sakamakon Karamar Hukumar Kogi

APC -14,168

PDP – 9,784.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin