✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direba a Fadar Shugaban kasa ya yi yunkurin kashe kansa

An ceto daya daga cikin direbobin da ake aiki a Fadar Shugaban kasa, mai suna Sunday Offre mai shekara 34, bayan da ya yi yunkurin…

An ceto daya daga cikin direbobin da ake aiki a Fadar Shugaban kasa, mai suna Sunday Offre mai shekara 34, bayan da ya yi yunkurin rataye kansa a wata bishiya. Offre dan Jihar Kuros Riba, ya fara aiki a matakin albashi na 3, inda ake biyansa Naira dubu 25. Ya  fara aikin ne a shekarar 2009, kamar yadda majiyarmu ta gano.

Wadansu daga cikin ma’aikatan Fadar Shugaban kasar sun bayyana wa  majiyarmu cewa, Offre mahaifin yara  biyu an same shi a cikin wani daji da ke yankin Unguwar Kubwa a Birinin Tarayya Abuja, a rataye yana lilo a bishiya da nufin kashe kansa.

Wannan al’amarin na Offre ya dauki hankali a Fadar Shugaban kasar. daya daga cikin abokan aikinsa ya ce an ceto shi ne a lokacin da uwargidansa ta samu rubutacciyar takardar da ya bar mata a kan tebur bayan ta dawo gida. “Sanarwar da uwargidan Offre ta yi a kan sakon da ya bari ga makwabtanta ne ya sa aka ceto rayuwarsa.”

Da jin wannan sanarwar ce sai makwabtan suka fara bincike ko’ina don sanin inda ya tafi ya rataye kansa. A lokacin da makwabtan suka samu direban a daure da bishiya sun yi tunanin ya rasu ne, har sun wuce da shi wajen adana gawa amma daga bisani suka fahimci ya fara motsa hannunsa Bayan ceto direban sai aka wuce da shi asibitin gidan Fadar Gwamnatin Tarayya don yi masa jinya. Ya dai fita daga cikin hayyacinsa na wasu kwanaki.

Binciken wakilinmu, ya gano an sallami Offre daga asibitin a karshen makon jiya.

A lokacin da Sakataren Gidan Gwamnati, Mista Jalal Arabi ya ziyarci Offre a asibiti, ya fara yi masa bayani a kan cewa, ba zai iya tuna abin da ya sa ya aikata hakan ba amma ya ce, “Ina dogaro da albashina ne kadai kuma ina cikin mawuyacin hali.” Sakataren ya shawarci direban da kada ya kara aikata irin wannan a rayuwarsa.