✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogara ga Ubangiji

A wannan mako za mu yi bincike ne a kan yadda za mu dogara ga Ubangiji cikin jarrabawar da muke fuskanta yau da kulum. A…

A wannan mako za mu yi bincike ne a kan yadda za mu dogara ga Ubangiji cikin jarrabawar da muke fuskanta yau da kulum. A takaice dai babu wani mai rai da zai ce bai taba fuskantar jarrabawa a rayuwarsa ba. Jarrabawa na zuwa mana ne ta hanyoyi daban-daban; takan iya zama ta bangaren rashin lafiya ko dukiya ko wurin aiki ko iyali da makamantansu. Abin tambaya a nan shi ne, jarrabawa na zuwa ga wanda ya yi zunubi ne kadai? Bari mu ga misali da rayuwar Ayuba a cikin Littafi Mai tsarki.

Ayuba 1:1-31, 6 -12; “Akwai wani mutum a kasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana kin aikata kowane irin mugunta.  Yana da ’ya’ya bakwai maza, mata uku. Yana da tumaki dubu bakwai da raƙuma dubu uku da shanu dubu daya da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a kasar gabas arziki nesa.”  6-12 “Sa’ar da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shaidan ma ya zo tare da su. Sai Ubangiji Ya tambaye shi, Ya ce, “Kai fa me kake yi?” Shaidan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko’ina a duniya.” Ubangiji Ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana kin aikata kowane irin mugunta.” Shaidan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maKa sujada? Ai, don ka kiyaye shi ne shi da iyalinsa da duk abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, Ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasar nan. Amma da a ce za ka raba shi da duk abin hannunsa, to, da zai fito fili ya zage ka kiri-kiri.” 

Ubangiji ya ce wa Shaidan, “To, shi ke nan, duk abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaidan ya tafi. 

A nan mun ga cewa Ayuba mutum ne mai tsoron Allah, natsattse, mai kin kowane irin mugunta yana kuma da arziki mai yawa, amma me ya faru? A aya ta 6 zuwa 12 mun ga cewa Allah Ya bai wa Shaidan damar jarabtan Ayuba. Abin lura a nan shi ne, duk jarrabawar da muke fuskanta a cikin rayuwarmu, Allah na sane da su, kada kuma mu ga cewa ai Allah ba Ya kaunarmu ba, sam. Allah ne Ya halicce mu, Shi Ya ba mu rai, Yana kuma da iko bisanmu. Sau da dama za ka ga mutane a cikin rashin sani idan abu ya faru da su misali mutuwar wani dan uwa, ko mu ce dukiyarsu ta kone a hadarin wuta, za ka ga suna kuka suna tambaya me ya sa Allah Ya bari abin ya faru da su? A ganinka abin da ya kamata su yi ko su fadi ke nan a irin wannan lokaci? Babu shakka irin wannan yanayi na da matukar zafi a zuci amma Ubangiji Allah Ya ce mana a Littafin 1 Korantiyawa 10:13 “Ba wani gwajin da ya taba samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan Adam ba. Allah Mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin karfinku ba, amma a game da gwajin sai Ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.” Tabbacin Yana da sanen duk matsalolin da muke ciki Ya kuma ba mu abin da zai taimake mu a irin wannan lokuta, wato maganarSa da saninSa. Sanin Ubangiji kadai zai sa mu gane kowane irin yanayi da muka fada ciki. Ishaya 41:13 “Ni ne Ubangiji Allahnku, Na karfafa ku, na kuwa fada muku, ‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.” Filibiyawa 4:6-8 “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roƙo, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukan fahimta, za ta tsayar da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.”  Zabura 50:15; “Ku yi kira gare Ni sa’ar da wahala ta zo, Zan cece ku, ku kuwa za ku yabe Ni.”

Bari mu dauki jarrabawa a matsayin matakala ce ta rayuwa ga sanin Ubangiji, a duk lokacin da muka shiga irin wannan yanayi. Shi ya sa ya kamata mu zama masu binciken Littafi Mai tsarki, muna nazari da kuma addu’a dare da rana ba tare da sai wani ya fada mana me ke cikinta ba. Domin rayuwa na nan ne kamar makaranta, a karshen kowane darasi malami yakan ba da jarrabawa don ya gwada dalibansa ko sun fahimci abin da suka koya. Wanda ya ci nasara akan ba shi lambar yabo, sannan wanda ya fadi yakan maimata darasin ko ya samu lambar faduwa, haka nan rayuwa take. Sai mu lura mu yi koyi da kowane irin jarrabawa da muke fuskanta a rayuwarmu, muna rokon Ubangiji muna kuma gode maSa a kowane yanayin da muka samu kanmu a ciki. 

Yakubu 1:2-4 “Ya ku ’yan uwana! Duk sa’ar da gwaje-gwaje iri-iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki kwarai. Domin kun san jarrabawar ban-gaskiyarku takan haifi jimiri. Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da komai ba.”

Ubangiji Allah Ya ba mu ikon dogara gare Shi, amin.