✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogara ya horar da matan da mazansu suka rasu noma kayan lambu

Shugaban Majalisar Wakilai, Barista Yakubu Dogara ya horar da matan da mazansu suka rasu da kuma matasa kan noma kayan lambu. Horarwar wadda aka yi…

Shugaban Majalisar Wakilai, Barista Yakubu Dogara ya horar da matan da mazansu suka rasu da kuma matasa kan noma kayan lambu. Horarwar wadda aka yi a karkashin kulawar Kwalejin Ilimin Koyar da Noman Kayan Lambu da Tsire-Tsire da ke dadin Kowa da kuma Ma’aikatar Gona ta Tarayya, ta gudana ce a karkashin shirin Shugaban Majalisar na ba da horo ga manoman da suke mazabarsa ta Dass da Tafawa balewa da kuma bogoro da nufin bunkasa harkokin noma a mazabar da Jihar Bauchi da Najeriya baki daya.

Da yake jawabi a wajen ba da horon a garin bogoro, Barista Yakubu Dogara ya ce wannan yana daya daga cikin abubuwan da yake ba da tallafi a kai domin yakar talauci da fatara da kuma yunwa a cikin al’umma.

Barista Dogara ya ce shirin tallafa wa noman zai yi tasiri a mazabarsa domin mafi yawan al’ummar da ke zaune a yankin manoma ne. Sai ya roke su da su yi amfani da irin horon da suka samu domin bunkasa sana’arsu da kuma wadata kasar nan da abinci.

Shugaban Majalisar wanda Mai tallafa masa ta fuskar watsa labarai, Mista Iliya Habila ya wakilce shi, ya bukaci wadanda suka ci moriyar shirin cewa kada su sayar da kayayyakin da aka ba su, ya kuma yi gargadin cewa za a binciki duk wanda ya sayar da nasa za a dauki matakin ladabtar da shi.

Wakilin Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Alhaji Hamza Shehu ya ce sun bai wa manoman horo ne kan noma kayan lambu da kuma sababbin dabarun shukar kubewa tun daga sharar gona da samar da iri da shuka da rainon irin da kuma girbe shi tare da adana shi don samun riba.

Sai ya gode wa Shugaban Majalisar Wakilan da kuma Ma’aikatar Gona ta Tarayya saboda ba da wannan tallafi da suka yi, wanda ya ce zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma tun daga yankunan karkara.

An bai wa wadanda suka ci moriyar shirin irin kubewa da injin feshin magani da taki na ruwa da maganin kwari da maganin ciyawa da tabarmar da za a rika shanya kayayyakin amfanin gonan da aka girbe don tsabtace shi da kuma kare tsakuwa daga shiga cikinsa da kuma kudin da za su fara gudanar da ayyukan noman da su.

Wadanda suka ci gajiyar shirin sun gode wa Shugaban Majalisar saboda wannan tallafi da aka yi musu suka kuma yi alkawarin yin amfani da sababbin dabarun noma kayan lambu da suka koya domin bunkasa sana’arsu.