✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana fita: An kama ababen hawa 307 a jihar Katsina

An kama ababen hawa 307 wadanda suka karya dokar hana zirga-zirga da gwamnatin Katsina ta kafa a fadin jihar da kuma ta rufe wasu kananan…

An kama ababen hawa 307 wadanda suka karya dokar hana zirga-zirga da gwamnatin Katsina ta kafa a fadin jihar da kuma ta rufe wasu kananan hukumpmi.

Daga cikin wannan adadi dai an kama motoci 159, kurkura 17 da babura 141 ana tuhumar su da karya dokar a wurare daban-daban wadanda kuma aka mika masu jan su ga kotun tafi-da-gidanka da aka kaddamar domin hukunta masu taurin kai.

Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isa ta ce an gurfanar da masu motoci 155, masu kurkura 17 tare da masu babura 106 a gaban kotun inda aka hukunta su bakin laifin da kowa ya aikata.

Hukuncin dai ya fara ne daga tarar N3,000 zuwa N10,000.

SP Gambo ya kuma ce, akwai masu motoci hudu da kuma masu babura 35 wadanda har yanzu ake cikin binciken su.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ta Katsina CP Sanusi Buba ya yaba da irin hadin kan da al’umma ke bai wa jami’an tsaro, ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da kiyaye doka da oda kamar yadda gwamnatin jihar ta shimfida a kokarin ta na yaki da annobar cutar coronavirus.

Kananan hukumomin da aka rufe dais u ne Daura, da Dutsinma, da Katsina, da Mani, da Safana, da Kankiya, da Matazu, da Musawa, da Jibiya da Batagarawa.