✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana fita: ‘Zaman gida ba abinci ba abin so ba ne’

Wasu daga mutanen Gombe sun bayyana rashin gamsuwa da matakin gwamnatin jihar na ayyana dokar hana fita. Gwamnatin ta dauki matakin ne dai bayan da…

Wasu daga mutanen Gombe sun bayyana rashin gamsuwa da matakin gwamnatin jihar na ayyana dokar hana fita.

Gwamnatin ta dauki matakin ne dai bayan da aka tabbatar da samun wadansu mutane da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.

Hajiya Hauwa Muhammad Inuwa na cikin wadanda suke ganin matakin ya yi tsauri.

“Matan da suke murna da wannan dokar ta zaman gida matan da mazajen su suke da wadata ne ba sa dawo wa gida a kan lokaci, ba su da kuma lokacin matan da ‘ya’yansu; amma idan miji ya dawo gida ba abin da za a ci ai ba abin murna ba ne saboda ba ni babu na yara wadanda idan suka ji yunwa za su bukaci abin da za su ci—idan babu ka ga rigima ta faru”, inji ta.

Hajiya Hauwa ta kuma ce ibada ma ba za ta yiwu yadda ya kamata ba saboda rashin kudi ko rashin abinci domin idan maigida ya wayi gari ya ga ba shi da abin da zai ci, yara suna masa kuka kuma ba damar fita sai ya ji tashin hankali.

Ita kuwa Helen Samsom cewa ta yi gaskiya ita kam ta ji dadin wannan dokar domin mazajen da suke kin dawowa gida su zauna da iyalansu yanzu an yi maganinsu kuma hakan zai sa yanzu su samu lokacin iyalan su.

“Da maigida sai a waya zai kira matarsa ya ce a dafa masa abinci kala kaza idan ya dawo gida lokacin yara sun yi barci shi kuma zai yi ta hira a kafar sadarwar zamani har ya yi barci bai samu lokacin matarsa ba, amma yanzu tun da yamma zai dawo gida ya zauna ya yi hira da iyalan nasa”, a cewar Helen.

Shi kuma wani matashi Ibrahim Sani cewa ya yi wannan dokar ta yi masa daidai domin an sa ta a lokacin da ake fara azumi kowa zai samu lokaci sosai na yi ibada ya kuma sha ruwa tare da iyalansa a gida ba a kan layi ba.

Kabiru Muhammad kuwa cewa ya yi wannan doka daidai take da an rufe mutane kirif domin menene amfanin a fita a yi zirga-zirga daga karfe 6 na yamma zuwa 7 na safe amma ba za a bude wuraren sana’a ba?

“Ta yaya za a hana mu sana’a bayan muna cikin kuncin rayuwa kuma ba a taimake mu ba ga shi an fara azumi? Gaskiya wannan dokar ba ta yiwu ba”, inji shi.

Shi ma wani alaramma da wakilin Aminiya ya zanta da shi a kan dokar rufe tsangaya da kuma mayar da almajirai garuruwansu cewa ya yi wannan doka tayi tsanani.

“Domin almajirai su ne idan bala’i ya faru suke addu’a Allah Ya kawo saukinta, amma ya za a yi yanzu da ake da bukatar addu’a kuma za a hana karatun almajirai?” Alaramma Yunusa Musa Bolari ya tamabaya.

Gwamnatin jihar Gombe ce dai ta ayyana dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 7 safe, sannan ta hana sallar jam’i da ma dukkan tarurrukan da suka kai na mutum biyu zuwa sama bayan wani taro da hukumomin jihar suka yi da shugabannin addini da sarakunan gargajia da kuma jami’an tsaro.