✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Hana Sallar Juma’a: An kama Limamai biyu a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta Kama malamai biyu a bisa karya dokar hana fita, inda har suka gudanar da sallar juma’a. Hakan na nuna cewa sun …

Gwamnatin Jihar Kaduna ta Kama malamai biyu a bisa karya dokar hana fita, inda har suka gudanar da sallar juma’a. Hakan na nuna cewa sun  bijirewa umarnin gwamnatin jihar na dakatar da  Sallar Juma’a saboda yaduwar annobar cutar Coronavirus

Gwamnatin Jihar Kaduna ta Kama malamai biyu a bisa karya dokar hana fita, inda har suka gudanar da sallar juma’a.

Kwamishinan Cikin Gida da Tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ne ya sanar da kama malaman biyu.

Ya kuma bayyana sunan malaman biyu kamar haka   Malam Aminu Umar Usman da Malam Umar Shangel, mazauna  Malali da Unguwan Kanawa a karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Kwamishinan, ya ce abin da suka aikata ya sabawa umurnin gwamnatin tare da shawarar da shugabannin addini suka bayar.

Ya kara da cewa gwamnati zata hukunta malaman dai-dai da abin da suka aikata.

Aruwan, ya ce gwamnati zata ci gaba da tabbatar da jama’a na bin dokar hana fita da kuma cinkoso domin kare yaduwar cutar coronavirus.

Ya kuma yabawa sauran jama’a da suke bin dokar da aka saka ta hanyar zama cikin gida.

Tun a makon jiya  gwamnatin jihar ta dakatar da Sallar Juma’a da taron addinai da addu’a a coci-coci. da sauran taruka jama’a a yunkurinta na dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar.