✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar haramta auren jinsi: Akwai gibi a tanadin?

Ni dai a rayuwata, ba zan iya tuna wata doka da ta tayar da kura ba kamar dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya  ba.…

Ni dai a rayuwata, ba zan iya tuna wata doka da ta tayar da kura ba kamar dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya  ba. Wannan doka da aka sanya wa hannu a bana, ta samu gagarumar amsuwa a nan cikin gida Najeriya amma kuma ta gamu da tofin Allah-tsine daga kasashen Turai da Amurka. Lallai abin na yi ne, a sanadiyyar wannan doka, sai ga shi mabiya manyan addinai biyu na Musulunci da Kiristanci sun sha inuwa daya, suna nuna gamsuwa da ita dari-bisa-dari!
Kamar yadda take, wannan doka ta tanadar da daurin shekara 14 ga duk wadanda aka kama da laifin auren jinsi daya ko gudanar da kungiya mai irin wannan manufa. Haka kuma ta tanadar da daurin shekara goma ga duk wanda aka kama da laifin bayyana irin wannan halayya ta tarayya da jinsi guda a bainar jama’a. Haka ma duk mutumin da ya hada kungiya ko kulob ko ya yi mata rijista, shi ma shekara goma zai kwasa a jarun. Ga wadanda suka daura irin wannan aure a kasashen waje kuwa, to idan sun shigo Najeriya, ba za a amince da hakan ba. Abin mamakin shi ne yadda giwayen kasashen yamma suka nuna rashin amincewa da dokar, inda suka ce wai an nuna wariya ga tsiraru, wanda haka ya saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
dan tsahirta mini ka ji wani zance, domin kuwa a yadda nake gani akwai gibi a cikin dokar nan. Har ma na tuno da a shekarun da suka gabata, yadda wata kungiya mai kare muradun auren jinsi daya ta durfafi Majalisar Tarayya, ta nuna adawa da ita wannan doka, a lokacin da ake kokarin tabbatar da samuwarta.
Wannan doka dai ta tabbatar da cewa duk wanda aka kama yana bayyana sha’awarsa ta aure ko makamancin haka ga jinsinsa a bainar jama’a, za a gargame shi na tsawon shekara goma. Abin tambaya a nan shi ne, to idan aka samu wani mutum a bainar jama’a yana nuna sha’awarsa karara ga karamin yaro fa? Domin dai na san zai yi wuya ga dan sanda a Najeriya ya iya tantance dangantaka tsakanin mutumin da yaron kai tsaye. Ma’ana ya iya gane cewa shin wannan da da uba ne ko kuwa? Koma dai yaya ke nan ya dace dan sandan ya turza ya iya tantancewa. Mafi yawan masu mu’amalar luwadi da kananan yara a Najeriya, suna yi ne a wajen gidajensu, sukan yi a ofisoshinsu ko wuraren shakatawarsu ko ta hanyar intanet da sauransu. Wannan dokar sam-sam ba ta ambaci irinsu ba. Wannan ya nuna cewa akwai gibi ke nan a nan.
Ya kamata kuma mu fahimta da cewa, a Najeriya ba ’yan luwadi da ’yan madigo ne kadai ke baje kolinsu a Najeriya ba; akwai masu jima’i da dabbobi, kamar kyanwa, karya, doki jaki da sauransu. Wannan doka sam ba ta ambata su ba balle ta tanadar da hukunci ga masu aikata laifin. Haka ma akwai masu jima’i da wasu abubuwa marasa rai, kamar ’yar tsana ko roba ko katako da sauransu. Su ma babu bayaninsu a dokar nan. Ya dace lallai a gyara wannan gibi, domin dokar ta cika daidai.
Kamar yadda na ambata a baya, ’yan luwadi da madigo fa ba su kadai ne ya kamata dokar nan ta tabo ba, domin akwai wasu salo-salo na jima’i da ba a yi la’akari da su ba. Akwai masu dukan yara ko ma baligan mutane, duka mai tsanani; wanda su a nasu tunanin, ta nan suke samun biyan bukata ta fuskar jima’i. Akwai ma mutanen da su da kansu ne suke son a doke su, inda ta nan ne suke samun dadi, kamar yadda mai jima’i ke ji. To ta yaya ’yan sanda za su gano haka, har su ce za su gudanar da bincike? Dokar nan dai ba ta ambata wannan  batu ba, wanda haka ya nuna mana cewa tana da gibi.
’Yan majalisunmu sun manta su tanadar da hukunci ga mutane masu aikata laifin labe. Abin nufi a nan shi ne, akwai wasu mutane da su kuma babu abin da ke burge su, kuma ta hanyarsa suke samun nishadi, shi ne ta hanyar labewa suna kallon wadanda ke jima’i ko kuma wadanda ke wanka ko shafa. A shekarun baya, a unguwar Nyanya-Abuja, an taba kama wani mutum yana leken wata mata tana wanka. Yana leken ne ta kofar makulli kuma ta haka ya ce yake jin dadinsa. Wannan ya nuna cewa lallai akwai masu aikata wannan laifi, wanda ya yi kama da na luwadi ko madigo.
Akwai ma wasu mutane, su babu abin da suke sha’awa sai su shiga cikin mutane suna yin wawan zama. Sai ka ga sun banzatar da tsiraicinsu mutane na kallo. Ta haka su kuma suke samun nishadinsu, wanda ya saba wa hankali. A manyan makarantunmu, hukumomi sun sha yin fada da ma’abota sanya suturun tsiraici. Ta yaya za a yi a ce wannan doka ta kawar da kai daga gare su? Shekaru nawa aka tanadar wa masu irin wannan dabi’a ta wawan zama ko gadarar nuna tsiraici?
Akwai masu laifin goge, inda za ka ga mutum a cikin taro ko zaman mota, yana goga jikinsa ga mace don ya samu nishadi. Wane hukunci kuma aka tanada ga masu laifin maganar lalata ta hanyar tarho ko intanet ko ta hotunan bidiyo? Akwai kuma matasan da ke yin jima’i ga tsofaffi, su kuma wane hukunci aka tanadar musu?
Idan har wannan doka za ta mance da irin wadannan masu laifi da aka ambata a baya, to lallai akwai sake, wai an ba mai kaza kai. Ya dace a koma baya a gyara.