Da Dumi Dumi

Dokar kiwo a Oyo: Za a ci tarar Naira dubu 500 ko daurin shekara 5 ga mai laifi

Kofar Majalisar Dokokin Jihar Oyo
Kofar Majalisar Dokokin Jihar Oyo

Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta kafa dokar hana kiwon dabbobi, inda ta tanadi tarar Naira dubu 500 ko daurin shekara 5 a gidan yari ga dukkan wanda ya karya dokar.

Shugaban Kwamitin Harkokin Gona na Majalisar Mista Peter Ojedokun ne ya gabatar da kudirin dokar gaban majalisar a ranar Alhamis ta makon jiya inda ya ce, kashi 98 cikin 100 na masu ruwa-da-tsaki kan kiwon dabbobi a Jihar Oyo sun amince da sabuwar dokar.

Aminiya ta ga hukuncin da ke cikin dokar da ke cewa: “Daga yanzu dukkan makiyayan da suke zaune a Jihar Oyo dole ne su mika kansu ga Ma’aikatar Gona domin yi musu rajistar bayan sun biya kudin katin shaida da za su rike kowane lokaci. Za a ci tarar Naira dubu 200 da daurin shekara 2 ga duk makiyayin da aka samu da laifin kin yin rajistar kansa kuma za a ci tarar Naira dubu 100 ko daurin shekara daya ga wanda bai mallaki katin shaida ba, kuma duk makiyayin da ya raunata wani mutumi zai biya tarar Naira dubu 500 ko daurin shekara 5, tare da biyan kudin jinya a asibiti ga wanda aka yi wa raunin. Kuma duk makiyayin da dabbarsa ta lalata amfanin gonazai biya diyya daidai da kiyasin da ma’aikatar ta yi.”

Dokar ta ce daga daga yanzu an hana kananan yara kiwon dabbobi a cikin dazuka sai dai idan suna tare da manya. Wanda ya taka wannan doka za a ci shi tarar Naira dubu 300 ko daurin shekara 3 a gidan kaso ko duka biyun.

Sabuwar dokar ta ce, daga yanzu an hana dukkan makiyaya da suka mallaki shanu ci gaba da kiwon dabbobi a cikin dazukan Gwamna sai idan sun nemi izini. “Duk wanda yake da sha’awar yin kiwo a cikin irin wadannan dazuka dole ne ya nemi izini daga gwamnatin jihar inda za ta ba shi damar yin kiwo na shekara 3 tare da sabunta wannan dama da izinin wanda ya mallaki dajin ko gonar,” inji dokar.

ADVERTISEMENT

Dokar ta umarci Ma’aikatar Gona ta kama dabbobin da aka gano suna kiwo barkatai a wuraren da aka hana tare da yin gwanjon dabbobin ga jama’a, inda za a zuba kudin cikin aljihun gwamnati. Kuma za a kafa hukumar hadin gwiwa mai kunshe da wakilan gwamnati da jami’an tsaro da kungiyoyi manoma da ta Miyetti Allah da jami’an sintiri da za su yi aikin tabbatar da wannan doka a jihar.

Yau mako biyu ke nan da shugabannin Fulani a jiha suka yi taro inda suka nuna rashin amincewa da sabuwar dokar, har suka yi barazanar zuwa kotu domin hana majalisar da gwamnati aiwatar da dokar da suka ce takurawa ce gare su da dabbobinsu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya