✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokta Rilwanu Lukman: Gwani a harkar man fetur ya kwanta dama

Da safiyar ranar Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa tsohon Ministan Albarkatun Man fetur Dokta Rilwanu Lukman rasuwa a birnin bienna fadar…

Da safiyar ranar Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa tsohon Ministan Albarkatun Man fetur Dokta Rilwanu Lukman rasuwa a birnin bienna fadar kasar Austeriya, bayan doguwar jinya, inda ya rasu yana da shekara 75.
 A lokacin rayuwarsa, ya rike mukamin Minista a gwamnatoci daban-daban kuma ya shafe shekara shida a matsayin Sakatare Janar na kungiyar kasashe masu Arzikin Man fetur (OPEC). Hakazalika, ya kuma shugabanci kungiyar a 1986 da 1989 da kuma 2002.
A wata sanarwa ta nuna alhininta game da rasuwarsa, kungiyar OPEC ta bayyana shi a matsayin gwarzo wanda ya sadaukar da rayuwarsa kan ci gaban kungiyar da ma al’ummar duniya baki daya.
An haifi marigayi Dokta Rilwanu Lukman ne a ranar 26 ga watan Agustan 1938, a birnin Zariya da ke Jihar Kaduna. Bayan ya halarci makarantar elimantare da sakandare, ya wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma Kwalejin Imperial da ke birnin Landan. Ya samu digirinsa na biyu a bangaren kimiyyar Hakar Ma’adanai a jami’ar ba da horo kan hakar ma’adanai ta kasar Austeriya a 1968.
A 1978, marigayin ya samu takardar shaidar digiri a fannin ilimin tattalin ma’adanai daga Jami’ar McGill da ke kasar Kanada da kuma digirin girmamawa daga Jami’ar Bologna da ke kasar Italiya.
Daga 1962 zuwa watan Maris din 2010, marigayin ya yi aiki da gwamnatocin gida da waje. Ya taba zama Ministan Ma’adanai da Makamashi  a 1984 zuwa 1985. Hakazalika ya zama Ministan Albarkatun Man fetur daga 1986 zuwa 1990. Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya taba nada shi mai ba shi shawara kan al’amuran da suka jibanci man fetur da makamashi daga 1999 zuwa 2007. Daga nan ne kuma marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa ya nada shi Ministan Albarkatun Man fetur wanda shi ne mukamin karshe da ya rike bayan Shugaba Goodluck Jonathan ya sauke su a shekarar 2010.
Shugaba Jonathan ya bayyana rasuwarsa da babban rashi kuma ya mika sakon ta’aziyya ga iyalansa da jama’a da kuma gwamnatin Jihar Kaduna. Sakon wanda babban mai magana da yawun Shugaban kasa, Dokta Reuben Abati ya sanya wa hannu, ya ce kasar nan ba za ta iya biyan marigayin ba, idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gabanta lokacin rayuwarsa. Har ila yau, Shugaban kasar ya ce ba za a manta da shi ba, saboda irin kyakkyawan wakilcin da ya yi wa kasar nan a kungiyar OPEC. A karshen sanarwar ya yi fatan Allah Ya saka masa da Aljannar  Firdausi.
“Alhaji Rilwanu Lukman ne Ministan Man fetur din da kasar nan ba ta taba samun irinsa ba a tarihi.” Wannan ne kalaman da tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi bayan samun labarin rasuwarsa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar a ranar Talata, inda ya bayyana rasuwarsa da babban rashi da kuma fatan Ubangiji Ya ba iyalansa da jama’ar kasar nan hakurin jure wannan rashi.
Gwamna Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya bayyana mutuwarsa da rashin da bai tsaya ga jama’ar Jihar Kaduna ko Najeriya kawai ba, amma na duniya baki daya.
kungiyar Gwamnonin Arewa ta bakin shugabanta, Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ta bayyana kaduwa da samun labarin rasuwar mamacin, inda kuma ta bayyana irin gudunmawar da ya bayar a bangaren man fetur da iskar gas da abin da kasar nan ba za ta manta da shi ba har abada.
A lokacin rayuwarsa, marigayin ya samu dimbin kyaututtukan yabo da dama daga ciki da wajen kasar nan.
A ta’aziyar Shugaban Majalisar Dattawa, Dabid Mark ya bayyana marigayin a matsayin dan kishin kasa kuma kwararren ma’aikaci da ya ba da gudunmawa wajen ci gaban kasar nan.
Marigayi Rilwanu Lukman ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya uku da kuma jikoki, za a ci gaba da tunawa da shi a bangaren man fetur da iskar gas din kasar nan da kuma yadda ya zama dan Najeriya na farko da ya jagoranci kungiyar OPEC.