Da Dumi Dumi

Dole mu gode wa Mourinho —Casillas

Golan Real Madrid Iker CasillasGolan kulob din Real Madrid da ke Sifen ya ce dole su gode wa tsohon kocinsu, Jose Mourinho bisa ga gudunma war da ya ba kulob din Real Madrid.
Mourinho ya lashe kofuna uku a lokacin da yake kocin kulob din, duk da cewa a shekararsa ta karshe ya mayar da Casillas benci, wanda hakan ya haifar musu da sa-toka-sa-katsi.
Casillas ya ce duk da haka ba za su ki yaba masa bisa gudunmuawar da ya ba kulob din Madrid ba.
Ya ce: “A yanzu dai na fara atisaye da Carlo, amma ban kai ga fahimtar bambancin da ke tsakaninsa da Mourinho ba. Ba maganar tuna baya ba ce, idan ma haka ne dole mu gode wa Mourinho bisa ga gudunmuwar da ya ba mu, yanzu dai burinmu shi ne kulob dinmu ya zama a sama.”
A karshe ya ce babu abin da ya sa a gaba kamar ya dawo matsayinsa na Golan farko a Madrid ba wai ya rika zaman benci ba.

Share