✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole Musulmi da Kirista su koyi hakurin zama da juna –Solomon Dalung

A makon jiya ne Ma’aikatar Harkokin Addini ta Jihar Bauchi ta shirya taron fahimtar da tsakanin limamai da malaman addinin Musulunci da kuma fastoci da…

A makon jiya ne Ma’aikatar Harkokin Addini ta Jihar Bauchi ta shirya taron fahimtar da tsakanin limamai da malaman addinin Musulunci da kuma fastoci da jagororin addinin Kirista don magance matsalolin zamantakewa a tsakanin mabiya addinai a jihar. Barista Solomon. Dalung Malami a Jami’ar Jos ya gabatar da takarda a wurin taron, kuma wakilinmu ya zanta da shi kan wannan yunkuri:

Aminiya: Ka halarci wannan taro da aka shirya wa fastoci don inganta zaman lafiya, wane jawabi ka gabatar?
Solomon Dalung: Taro ne da gwamnatin Jihar Bauchi ta shirya don a samu tuntubar juna a tsakanin malaman addinin Musulunci da na Kirista, kuma a matsayina na Babban Bako Mai jawabi, na farko na gabatar da kasida ne kan zaman lafiya da hadin kai da lura da rigingimu a lokacin da kasa ta samu kanta a ciki. Na lura da halin da muke ciki a kasar nan ya nuna ba ma koyi da abin da ya samu wasu kasashe irin su Somaliya da Libya game da rigingimu. Don haka na jawo hankalin shugabanni da a koma kan koyarwar Littafin Allah don a samu kauna da zaman tare don a samu zaman lafiyarmu da na addini. A bincikena na fahimci duk rigingimun da aka samu a kasar nan ba su da nasaba da addini, sai dai game da yanayin siyasar kasa da kuma rashin hakurin zama da juna. Don haka da limamai da fastoci da malaman kowane addini Allah Ya ba su albarka da amanar su lura da wannan dama su daidaita halin zaman mutanensu. Na kuma bayyana cewa cin hanci da rashawa da satar kuri’u a lokacin zabe ko magudin zabe su ne suka kawo tarnaki a lamurran gwamnati. Don haka ina mai ra’ayin dole a kawo hukunci mai tsanani kan masu magudin zabe da satar dukiyar kasa a cikin gwamnati. Ya kamata hukuncin ya zamo na kisa don ya zamo ishara ga kowane mai satar dukiya ya galabaita gwamnati, ya nakasa jama’a da ci gaban kasa. Kuma na kirayi jama’ar Musulmi su daina amfani da kalmar kafirci a kan Kirista su rika kiransu da sunan da Allah Ya kira su na Ahlul Kitabi don suna da littafi ba kafirai ba ne. Domin wannan yana kawo rura wutar gaba da kiyayya a tsakanin juna, don haka ya kamata kowa ya gyara kuskurensa a fahimci juna a zauna tare lafiya kamar yadda Allah Ya zuba mu a cikin kasar nan.
Aminiya: Wato kana ganin yi wa juna adalci a tsakanin Kirista da Musulmin Najeriya zai kawo zaman lafiya ke nan?
Solomon Dalung: Yi wa juna adalci ya zamo dole, don kowa ya samu kwanciyar hankai. Ko a cikin laccar da na gabatar na bayar da misalin wani Musulmi da aka bukaci ya kawo wanda zai yi wani aiki a Fadar Shugaban kasa, amma sai ya mika sunana. Musulmi ne ban sani ba, shi ne na tambayi Kiristoci tunda Musulmi zai yi haka ya kamata su ma su kamanta don na san su zai yi wahala su kawo sunan Musulmi idan an nemi su kawo wanda zai yi irin wannan aiki. Na kawo ne don bayyana cewa idan Musulmi zai yi haka, mu ba za mu iya ba, to, ya kamata mu koma mu yi koyi da juna. Abu ne da zai karfafa zaman tare.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da Dokar Ta-baci da ake fama da ita a wasu jihohin Arewa da kuma yadda kake ganin za a samu maslaha kan matsalar Boko Haram?
Solomon Dalung: Dokar Ta-baci ba za ta kawo zaman lafiya ba, sai dai ta karya garkuwar ’yan tsageru masu fito-na-fito. Domin Boko Haram suna kai hare-hare kuma yanzu an nakasa su, gwamnati ta kawo matsala kan wannan saboda ba a tunanin wace hanya za a bi don magance musu matsalarsu. Da wadanda suka rasa iyaye da dangi ta wannan hanya da wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba aka kashe su. Da kuma wadanda aka kama da rai, wane shiri za a yi a gyara su ko a daidaita da su, duk ba mu ga wani shiri kan wannan ba tukun, wanda kuma yin hakan ya zamo dole idan ana son komai ya kare. Idan an tafi a haka tsugune ba ta kare ba.
Aminiya: To mene ne matakin da kake gani za a dauka don daidaita al’amura?
Solomon Dalung: Abin yi shi ne gwamnati ta dawo ta hada Kirista da Musulmi da wannan abu ya shafa da wadanda aka kai musu hari da wadanda aka kama da wadanda aka lalata musu dukiya ko aka kashe musu dangi, a zo a hada har da ’yan Boko Haram a zauna a daidaita a nemi sulhu da yafe wa juna. A dauki kudin kasa a lissafa asarar da kowa ya yi a biya shi diyya shi ne zai sa kowa ya san cewa gwamnati ta damu da shi. Amma idan aka ce an kashe wa mutum iyaye da dangi an bar shi maraya ko an kama wani nasa an kashe haka kurum ya tashi ba mai taimakonsa, to idan ya tashi zai iya daukar makami shi ma ya ci gaba da gwagwarmayar yakar kasar. Kuma idan ba a yi sulhu ba, duk abin da aka yi wallahi tallahi damuwa ba za ta kare daga gare mu ba, sa dai idan an toshe nan can ya bude.