✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

..Dole Saudiyya ta kawo gawar Khashoggi – Majalisar Dinkin Duniya

Shugabar Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet na kara matsa wa kasar Saudiyya lamba, ta bari masu bincike na kasashen…

Shugabar Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet na kara matsa wa kasar Saudiyya lamba, ta bari masu bincike na kasashen waje su shiga tawagar da ke binciken mutuwar.

Miss Bachelet ta kuma bukaci hukumomin Saudiyyar su bayyana inda gawar mamacin ta ke don a samu damar gudanar da bincike a kai.

Mai magana da yawun hukumar, Rabina Shamdasani ta bayyana damuwar da suke yi kan batun, ta kuma ce bai kamata a bar Saudiyya ta gudanar da binciken ita kadai ba.

Hukumar ta yi kira ga kasashen Turkiyya da Saudiyyar su bada hadin kai wajen binciken, sannan hukumomin Saudiyya su fadi inda gawar mista Khashoggi take, saboda duk wani bincike ba zai kammalu ba tare da an yi kwakkwaran bincike kan gawarsa ba.

Masu bincike a Turkiyya sun nace da suna so a bar su su bincika wata rijiya da ke gidan Jakadan Saudiyya wanda ba shi da nisa da ofishinsu, amma har yanzu hakan ba ta yiwu ba.