✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don Jazzy ya mika kyautar ban mamaki

Duk da cewa halinsa ne yin kyauta ga mabukata da kuma masoyansa, amma a makon da ya gabata, shahararren furodusan wakokin zamani, Don Jazzy ya…

Duk da cewa halinsa ne yin kyauta ga mabukata da kuma masoyansa, amma a makon da ya gabata, shahararren furodusan wakokin zamani, Don Jazzy ya mika wata kyautar ban mamaki ga wani masoyinsa.
Don Jazzy, wanda shi ne kashin bayan tallafa wa shahararen mawakin nan na zamani, Dbanj har ya yi suna, ya saba da raba kudi da bayar da gudunmowa ga cibiyoyin agaji, kamar kuma yadda yake yawan kyautar katin waya ga masoyansa. A makon da ya gabata ne kawai ya duba turakarsa ta Twitter, sai ya ga wani masoyinsa ya rubuta digon aya (.) kawai a shafin nasa, maimakon ya rubuta wasu kalmomi. Wannan abu ne ya ja hankalinsa, kawai sai ya ce masa ya aika masa da lambar asusun ajiyarsa na banki. Take kuwa ya tura masa da kyautar Naira dubu 100.
Kamar yadda abin ya faru, a ranar 1 ga wannan wata ne, da misalin karfe 1:37 na rana, sai wani masoyin Don Jazzy, mai suna Michael Collins ya tura sakon digon aya (.) ga turakarsa ta Twitter @DONJAZZY.
Shi kuwa Don Jazzy na budewa ya ga wannan digon aya, a daidai karfe 1:39 na ranar, sai ya rubuta masa cewa: “Ka kuwa yi dacen samun kyautar Naira dubu 100, domin kai ne mutum na farko da ya fara rubuta mani digon aya.”
Daga nan ne kuwa ya nemi ya tura masa lambar asusun ajiyarsa, bayan ya tura, shi kuwa ya aika masa wadannan kudi, Naira dubu dari daya cif.
Shi kuwa wanda ya yi dace da wannan garabasa, cikin murna, daidai misalin karfe 2:52 na ranar ya rubuta kalmomin godiya, kamar haka: “Ina yi maka matukar godiya Don Jazzy saboda wannan kyauta ta Naira dubu 100 da ka turo mani. Ina godiya dan uwana, Allah Ya yi albarka!”