✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta sake kame Sowore bayan wani gumurzu da suka yi da magoya bayansa a Kotu

Cikin kasa da awa 24 da Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sake kama Omoyele Sowore bayan ta tsare shi na tsawon kwanaki…

Cikin kasa da awa 24 da Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sake kama Omoyele Sowore bayan ta tsare shi na tsawon kwanaki 124, jami’an DSS sun kara yin awon gaba da shi ne bayan yaje sauraren zaman da babbar kotun tarayya da ke Abuja tayi yau, domin dage zaman sauraron karar.

Alkalin kotun Jastis Ojukwu, ya dage zaman sauraren shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Fabarairun shekarar 2020, bayan zaman kotun sai jami’an DSS din suka yi yunkurin sake kame Sowore lamarin da ya sanya magoya bayansa da lauyoyinsa suka nuna turjiya inda suka nuna cewa, jami’an tsaron basu da hurumin kame shi a cikin harabar kotun.

A karshe jami’an na DSS sun yi awon gaba da shi zuwa ofishin su a cikin motar babban lauyansa Femi Falana, bayan sun yi yarjejeniyar cewa jami’in DSS ne zai tuka motar tare da babban lauyan nasa zuwa ofishin hukumar inda jami’an na DSS suke biye da motar a cikin motocin su.

Hukumar DSS ta ce, ta tsare Sowore ne saboda zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon kiran juyin juya hali da ya yi – ya yi masa lakabi da #RevolutionNow.

Sowore a Kotu