Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Dubbai sun mutu a mahaukaciyar guguwar kasar Filifins 1

Dubbai sun mutu a mahaukaciyar guguwar kasar Filifins 1

Birnin Samar ne nan a kasar Filifins, guguwa ta daidaita shiA Juma’ar da ta gabata ce al’ummar kasar Filifins suka wayi gari da mahaukaciyar guguwa, wacce ta daidaita sassan kasar, inda dubban mutane suka mutu, wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.

Hukumar Agajin Gaugawa ta Majalisar dinkin Duniya ta tabbatar da ccewa sama da mutane miliyan sha daya ne guguwar ta shafa, inda gidaje sama da dubu 700 suka ruguje.
Guguwar, wacce aka yi wa lakabi da ‘Haiyan’ an kyautata zaton ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane dubu 10, inda adadin kuma yake karuwa.
Babbar jami’ar Hukumar Agaji ta Majalisar dinkin Duniya, beleri Amos tuni ta isa kasar Filifins domin jagorantar sauran jami’ai domin ci gaba da aikin ceto da tallafa wa jama’ar da guguwar ta shafa.
Ta bayyana wa rediyon BBC cewa, guguwar ta yi muguwar barna fiye da kima, inda dubban mutane suka shiga matsala mai girma. “Suna bukatar abinci, suna bukatar ruwan sha; jama’a na neman tallafi da kariya.” Inji jami’ar, a yayin da take bayani game da ta’adin mahaukaciyar guguwar.
Babbar jami’ar kuma ta bayyana cewa akwai tsananin bukatar karin jirage masu saukar angulu domin ci gaba da rangadin yankunan kasar, da nufin gano irin ta’adin da guguwar ta haifar. Ta ce Majalisar dinkin Duniya za ta hada hannu da gwamnatin Filifins domin agaza wa al’ummar kasar. “Za mu fi maida hankali wajen samar wa jama’a abinci, magani da tsaftataccen wuri da kuma kwashe baraguzan gine-gine da guguwar ta warwatsa, sannan kuma da bayar da agajin gaugawa ga mutanen da suka jikkata.” Inji jami’ar.
A yayin da Majalisar dinkin duniya ta kaddamar da asusun tallafi na Dala miliyan 301, ya zuwa yanzu dai, ana ci gaba da samun tallafin kudi, abinci da sauran kayan agaji daga kasashen duniya, inda majalisar ta bayar da Dala miliyan 25 domin bayar da agajin gaugawa ga mutanen da abin ya shafa.
Sakataren Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya bayyana barnar da guguwar ta yi da cewa, “al’amari ne mai karya zuciya.”
kasar Amurka za ta bayar da tallafin Dala miliyan 20, a yayin da kasar Jafan ta bayar da tallafin Dala miliyan 10, kamar kuma yadda ta alkawarta aikawa da kayan abinci da sauransu. Ita ma kasar Ostraliya, Dala miliyan dubu 9.6 ta bayar a matsayin tallafi. Gwamnatin kasar China, wacce wasu ’yan kasarta ke ganin kamar ta kasa, ta yi alkawarin bayar da tallafin Dala dubu 100, gami kuma da wata Dala dubu 100 ga kungiyar Red Cross ta kasar China, domin bayar da tallafi ga mutanen da suka jikkata.