✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubi kan nazarin Hausa da Hausa (2)

Ci gaba daga makon jiya Misali akwai lokacin da aka gayyaci wani wanda ya karanta Hausa ganawa ta daukar aiki a gidan wata jarida ta…

Ci gaba daga makon jiya

Misali akwai lokacin da aka gayyaci wani wanda ya karanta Hausa ganawa ta daukar aiki a gidan wata jarida ta Hausa, kafin ya halarci ganawar sai da aka kira shi ya zauna ya rubuta wata ’yar kwarya-kwaryar jarrabawa da ta kunshi fassara, bayan ya kammala ne aka sanar da shi cewa za a kira su domin manyan kamfanin jaridar za su gana da su dai-dai-da-dai-dai. Nan take cikinsaya duri ruwa, ya rika tambayar cewa “Da Hausa za a yi ganawar ko da Ingilishi?”

Da ya ji cewa da Ingilishi ne za a yi sai gabansa ya fadi saboda ya san yana da matsala a bangaren Ingilishi. A ranar da aka gana da su din ya kasa tabuka komai, saboda ya kasa yin bayani da Ingilishi. A karshe dai ya kasa samun nasara, saboda tun a wurin fassarar da ya rubuta ya yi ta tafka shirme, sannan a wurin ganawar da aka yi da shi ya kasa  bayani sosai, dole aka dauki wanda ya karanta fannin kimiyya aka bar shi, domin shi ya iya Ingilishi kuma ya yi bayani sosai a wurin ganawar sannan kuma fassarar da ya yi ta fi ma’ana.

Haka kuma an taba tura wani wanda ya karanta Hausa gidan jaridar Hausa domin ya yi aikin hidimar kasa, a ranar farko sai aka ba shi ra’ayin Edita na Ingilishi domin ya fassara, amma da ya fita ba a sake ganinsa ba, sai bayan wasu kwanaki ya bugo ya sanar da cewa an canja musu wurin aiki. Ashe wannan aikin fassarar da aka ba shi ya tsorata shi ne shi ya sanya ya gudu.

A baya masanin harshen Hausa babu inda ba zai yi aiki ba, saboda gwani ne a bangaren Hausa da Ingilishi, shi ya sanya yake iya rike mukamai iri-iri kuma ya ba da mamaki. Misali Farfesa Bello Salim, na Jami’ar Bayero da ke Kano, masanin harshen Hausa ne, lokacin da ya shugabanci Hukumar Jarrabawar Shiga Jami’o’i (JAMB) ya bayar da mamaki saboda irin abubuwan da ya yi, haka kuma Farfesa Dandatti Abdulkadir, shi ma masanin harshen Hausa ne wanda kuma ya zama Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, hatta Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano da ya yi suna kwanakin baya a jihar saboda yaki da miyagun kwayoyi Mohammed Wakili (Singham) Hausa ya karanta. Akwai ire-irensu da dama da suka yi fice a bangarori da dama na rayuwa, kuma masu digiri a Hausa sun yi fice sosai a kafofin watsa labarai na ciki da wajen kasar nan. Sai dai abin takaici yanzu masana harshen Hausa masu digiri na farko suna da matsalar shiga ko’ina su yi aiki saboda raunin da suke da shi a bangaren Ingilishi.

Saboda haka ya kamata jami’o’i da kwalejojin ilimi su bayar da fifiko wajen nazarin harshen Ingilishi  ga mai karanta Hausa kamar yadda ake yi ga harshen Hausa, saboda tare suke tafiya domin Ingilishi ne harshen gwamnati, kuma ba zai yiwu a yi fassara mai kyau da Hausa ba sai an fahimci Ingilishi sosai. Zai yi kyau idan aka samar da wani darasi ga daliban Hausa a kan Ingilishi da za a hada da sauran darussan da daliban suke karantawa, haka kuma a daure a hada koyar da daliban Hausa fassara daga Hausa zuwa Ingilishi, maimakon daga Ingilishi zuwa Hausa kawai da ake yi a mafi yawan jami’o’i da kwalejojin ilimi. Ta haka ne daliban harshen Hausa za su kara kwarewa a harsuna guda biyun kuma su zama gwanayen fassara na duka harsunan.

Tun da Ingilishi harshen mu’amala ne na kasar nan, bai dace a bar daliban harshen Hausa a baya ba wajen fahimtarsa, domin har yanzu nazarin Hausa da ake yi a matakan digiri na biyu zuwa sama mafi yawansa da Ingilishi ake yi. Idan a kasar waje ne kuma za a yi karatun duk dai da Ingilishi ne za a yi.

Saboda raunin da wadansu masu digiri a Hausa suke da shi ne ya sanya ba su iya yin wani aiki sai dai koyar da harshen Hausa a makarantun sakandare zuwa kasa. Idan kuwa har aka dauke su aiki a wasu bangarorin to karshenta a ji kunya. Wannan ne ya sanya ake yi wa mai digiri a Hausa kallon raini. Ko da yake akwai kuma dabi’ar nan ta dan Afirka na rashin daraja kayansa, ya fi ganin kimar kayan Turawa fiye da nasa.

Domin haka ya kamata masana Hausa masu digiri na farko zuwa kasa su rika fahimtar Ingilishi sosai yadda za su iya aiki a ko’ina ba tare da shakkar komai ba, domin bai kamata a ce wadanda suka karanta wasu fannonin ilimi su ne suke mamaye kafofin watsa labaran da suke amfani da harshen Hausa maimakon masu digiri a harshen Hausa da su ne ya kamata su zama jagororinsu ba.