✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk dan Arewa dan Arewa ne a wurin mutumin Kudu – Ambasada Kwande

Tsohon Jakadan Najeriya  a kasar Switzerland Ambasada Yahaya Kwande, ya  ce duk wani dan Arewa idan ya je Kudancin kasar nan daga kowace kabila yake,…

Tsohon Jakadan Najeriya  a kasar Switzerland Ambasada Yahaya Kwande, ya  ce duk wani dan Arewa idan ya je Kudancin kasar nan daga kowace kabila yake, ana daukarsa dan Arewa ne kawai.

Ambasada Yahaya Kwande ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron da Kungiyar Dalibai ta Tunawa da marigayi Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato reshen Jami’ar Jos, ta shirya a garin Jos.

Ya ce duk wani kabilar Arewa idan ya je Kudu suna daukarsa dan Arewa ne Bahaushe ko ba Bahaushe ba don haka Arewa ta dukkan kabilun Arewa ne baki daya.

Ya ce lokacin marigayi Sardauna kowace kabila mutumin Arewa ya fito yana son a ce masa dan Arewa, ko Kirista ko mai bin addinin tsafi ne, kowa yana takama a kira shi dan Arewa.

“Marigayi  Sardauna ya rike dukkan al’umman Arewa ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Akwai lokacin da ya debi mutum 16 daga Arewa ya tura Kano, don su koyo aikin likita, daya daga cikinsu Dokta Pam daga Jos ya dauko shi. Sai ya fadi jarrabawa sai aka je aka fada masa. Nan take ya ce bai fadi ba, ya ce malamin ne ya fadi. Ya ce a mayar da shi makarantar a koya masa sai ya iya. Aka mayar da Dokta Pam, a karshe sai da ya zama Shugaban Likitocin Najeriya baki daya,” inji Kwande

Ambasada Kwande ya yi bayanin cewa lokacin da Sardauna yake raye babu inda yake so ya zo ya huta kamar Jos, “A kullum yana cewa babu garin da yake son ya rayu, idan ya yi ritaya kamar Jos.”

Ya ce mutanen Arewa mutane ne masu mutunci, “Don haka kada mu yarda a rika raba mu. Domin hadin kan da muke da shi a da ne ya sa muka gagari kowa a Najeriya,” inji.

A nasa jawabin Mai martaba Sarkin Wase Alhaji Muhammad Sambo Haruna ya yaba wa daliban Jami’ar Jos da shugabannin jami’ar kan kokarin da suka yi wajen kafa wannan kungiya.

Sarkin Wase wanda Galadiman Wase ya wakilta, ya bayyana cewa marigayi Sardauna mutum ne mai son al’umma ba tare da bambancin kabila ko addini ba.

Ya yi kira ga daliban da suka kafa kungiyar su ci gaba da koyi da marigayin ta hanyar rungumar al’umma ba tare da bambancin addini ko kabila ba.

Tun farko a jawabin Shugaban Kungiyar Daliban ta Tunawa da Sardauna, a Jami’ar ta Jos, Sardauna Haruna Yusuf Abba ya bayyana cewa sun shirya taron ne, don tunawa da halayen kirki da abubuwan koyi da marigayi Sardauna ya bar wa al’ummar Arewa.

Ya yi kira ga daliban jami’ar su zo su hada kai don warware matsalolin da suke damun Arewacin kasar nan, na rashin tsaro da talauci da rashin ilimi.

A wajen wannan taro wanda ya samu halartar manyan mutane daga wurare daban-daban, an gudanar da  wasannin kwakwayo kan muhimmancin hadin kai, tare da nade-naden sarautun gargajiya.