✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk dan kwallo na sha’awar Real Madrid – Pogba

Paul Pogba ya bayyana Real Madrid a matsayin kungiyar da kowane dan wasa zai yi fatan zuwa, amma kuma ya ce yana jin dadin zamansa…

Paul Pogba ya bayyana Real Madrid a matsayin kungiyar da kowane dan wasa zai yi fatan zuwa, amma kuma ya ce yana jin dadin zamansa a Manchester United.

Dan wasan na tsakiya mai shekara 26 ya yaba wa kocinsu na rikon-kwarya Ole Gunnar Solskjaer, amma ya ce Real Madrid kungiya ce wadda duk wani yaro ko wani dan kwallon kafa yake burin zuwa.

A wani taron manema labarai a Faransa Pogba ya ce: ‘’ Tana daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya. A koyaushe ina fadin cewa Real Madrid kungiya ce da kowane dan wasa ke fatan taka wa leda.’’

Sai dai ganin yana yabon kungiyar ko yana son tafiya can ne, sai ya ce;  “A yanzu dai ina farin cikin kasancewa a Manchester United. Ina wasa, ga kuma sabon koci.’’

Pogba zai buga wa Faransa wasan neman gurbi a gasar cin Kofin Turai ta 2020 da za su kara da Moldoba a yau Juma’a sannan kuma ranar Litinin su fafata da Iceland.

Kuma Pogba ya kara da cewa kocin rikon-kwayar na Manchester United ya cancanci a bar masa aikin horar da kolub din.

Shi dai Paul Pobga idan ba a manta ba, ci gaba da zamansa a Manchester United ya kasance cikin rashin tabbas a lokacin da yake sa-in-sa da tsohon kocinsa Jose Mourinho, wanda Solskjaer ya maye gurbinsa a watan Disamba.

Zuwan Solskjaer kungiyar ya zo daidai da farfadowar dan wasan, wanda ya ci kwallo hudu a wasansa uku na farko a karkashin sabon kocin.

Kocin mai shekara 46 ya kulla yarjejeniyar zama a kungiyar har zuwa karshen kakar da ake ciki, amma Pogba ya ce mai horar da ’yan wasan ya yi kokarin da ya kamata a ba shi aiki na dindindin.

Pogba wanda yake da kwantiragi da United har zuwa shekara ta 2021 ya ce ‘’ba shakka muna son ya tsaya.’’

Ya ce: “Sakamakon da muke samu yana da kyau. Ina da kyakkyawar alaka da shi. Yana da kyakkyawar alaka da ’yan wasa. Idan dan wasa yana jin dadi, yana son a ci gaba da tabbatar da farin cikin nan nasa. Solskjaer ya cancanci aikin. Ya san kungiyar, ya san komai game da kungiyar.”

‘’Koci ne mai kyau da ke bai wa ’yan wasa kwarin gwiwa. Wannan ne yake ba mu ’yancin wasa cikin jin dadi, saboda kila mun rasa wannan saboda irin sakamakon da muke samu a da.’’ Kamar yadda BBC ta ruwaito daga jawabinsa.

Lokacin da aka kori Mourinho, United tana matsayi na shida a teburin gasar Firimiya ta Ingila, maki 11 tsakaninta da ta hudu, amma yanzu ita ce ta biyar, da tazarar maki uku tsakaninta da Tottenham ta uku.

Haka kuma United din ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar Kofin Zakarun Turai, bayan da ta doke kungiyar Paris St-Germain ta kasar Faransa.

Pogba ya kara da cewa: ‘’A yanzu mun fi da kuma sakamakon yana kasancewa mai kyau sosai.’’