✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duniya ta yi tir da hukuncin da aka yanke wa makasan Khashoggi

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya mai bincike kan kashe-kashen babu gaira babu dalili, Misis Agnes Callamard, da kasar Turkiyya da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na…

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya mai bincike kan kashe-kashen babu gaira babu dalili, Misis Agnes Callamard, da kasar Turkiyya da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasashen duniya, sun yi tofin Allah tsine kan hukuncin da wata kotun Saudiyya ta yanke game da kisan da aka yi wa dan jaridar nan dan kasar Saudiyya a bara, Jamal Khashoggi, suna cewa kasar ta kasa tabbatar da adalci.

Sai dai duk da kakkausar sukar da duniya ke yi wa hukuncin, wani jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya yi maraba da hukuncin yana cewa “Wani muhimmin mataki ne” wajen tabbatar da an hukunta masu hannu a kisan gillar.

Turkiyya

Turkiyya ta kwatanta hukuncin a zaman “wata babbar badakala” tare da fadin cewa ainihin wadanda suke da hannu dumu-dumu a kisan gillar an ba su kariya.

“Wadanda suka aika da tawagar ’yan ina-da-kisa zuwa birnin Istanbul a wani jirgi na musamman… kuma suka nemi shiririntar da batun kisan gillar, an ba su kariya,” kamar dai yadda babban jam’in watsa labarai na Shugaba Recep Tayyip Erdogan, Mista Fahrettin Altun, ya rubuta a shafin Twitter.

Majalisar Dinkin Duniya

Agnes Callamard, wadda jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ce ta musamman kan kisan gilla, wacce a baya kai-tsaye ta alakanta Yarima Mohammed Bn Salman da kisan Khashoggi, ta ce hukuncin “ba komai ba ne illa rashin adalci.”

“A karkashin dokokin duniya, kisan da aka yi wa Khashoggi kisan ne wanda babu adalci a ciki, wanda kasar Saudiyya ke da hannu a ciki,” kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

Amurka

A nata bangaren kasar Amurka maraba da hukuncin ta yi, inda ta kira hukuncin da ‘muhimmin mataki’.

“Hukuncin na yau, muhimmin mataki ne wajen tabbatar da an hukunta wadanda suke da hannu dumu-dumu a wannan mummunan al’amari na kisan gilla,” kamar yadda wani jam’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya fada wa manema labarai jim kadan bayan hukuncin.

Amurkar ta kuma “Karfafa gwiwar mahukuntan Saudiyyar wajen tabbatar da an bi matakan shari’ar cikin adalci,” kamar yadda jami’in ya nuna.

Kungiyar Reporters Without Borders

Kungiyar Reporters Without Borders mai mazauni a birnin Paris da ke sa ido kan hakkokin ’yan jarida a duniya ta ce “An take hukunci da adalci a shari’ar,” hukuncin kisan da aka yanke bayan shari’ar da ba ta mutunta ka’idojin shari’a na duniya ba.

Babban Sakataren Kungiyar, Christophe Deloire, ya wallafa a shafin Twitter cewa hukuncin “za a fassara shi ne a matsayin hanyar da za a rufe bakin wadanda ake zargi, ta yadda za su daina magana a kan batun, domin kawai a yi rufa-rufa wajen bayyanar da gaskiyar al’amari.”

Amnesty International

Kungiyar Amnesty International ta yi kakkausar suka game da hukuncin inda ta ce “Wani tsabagen rashin adalci ne wanda bai samar da adalci ko kuma ya tsage gaskiyar al’amari ga  Jamal Khashoggi da masoyansa ba.”

“Lura da rashin gaskiya daga hukumomin Saudiyya da kuma rashin kwakkwarar Ma’aikatar Shari’a mai cin gashin kanta, binciken kasa-da-kasa mai zaman kansa kuma marar bangare ne kawai zai tabbatar da samar da adalci ga Khashoggi,” inji Daraktar Nazari ta Kungiyar a yankin Gabas ta Tsakiya, Lynn Maalouf.

“Hukuncin ya gaza bayanin hannun mahukuntan Saudiyya game da wannan mummunan batun mai matukar tayar da hankali ko kuma ya yi karin haske kan ko ina gawar Jamal Khashoggi take,” ta fada a wani jawabi.

Hatice Cengiz (Matar da ya so ya aura)

Hukuncin ya sanya budurwar Khashoggi, Hatice Cengiz cikin yanayin na rashin gamsuwa, inda ta wallafa a shafin Twitter cewa “Sanarwar Saudiyyar ba abin a yi na’am da shi ne ba.”

Birtaniya

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Dominic Raab ya yi tir  da hukuncin inda ya ce “Yin amfani da hukuncin kisa kan kowane batu a zaman tsarin hukunci”.

“Kisan Jamal Khashoggi babban laifi ne,” kamar yadda Raab ya fada cikin wata sanarwa. “Iyalin Mista Khashoggi suna da ’yancin ganin an yi adalci game da kisan rashin imanin da aka yi masa. Lallai ne Saudiyya ta tabbatar da dukkan masu hannu a aika-aikar sun fuskanci hukunci kuma ta tabbatar ba a sake aikata lamari makamancin haka ba a nan gaba.”

Salah Khashoggi

Dan marigayi dan jaridar, Salah Khashoggi, ya ce iyalansa sun samu adalci, godiya ga Babban Mai shigar da Kara na Kasar Saudiyya.

“A yau a matsayinmu na ’ya’yan wanda aka yi wa kisan gilla, Jamal Khashoggi, cikin kaddarar Allah, an yi mana adalci. Muna kara jaddada kwarin gwiwarmu ga tsarin shari’ar kasar Saudiyya a kowane mataki, kasancewar sun yi mana adalci kuma an samu daidaito a hukuncin,” ya fada a wani sakon shafin Twitter.

Karen Attiah

Abokiya ga Khashoggi kuma Edita a jaridar Washington Post, ta ce shari’ar gaba dayanta “wani abin kunya ne.”

“Hukuncin da aka yanke musu kan kisan gilla marar ma’ana mai cike da tashin hankali kan Jamal Khashoggi, bai kai na wanda aka yi wa Jamal Khashoggi ba,” ta ci gaba da cewa “Ci gaba da kashe rayuka ba zai zama mafita ba. Shari’ar kanta a asirce aka yi ta. Iya abin da muka sani wadannan mutane biyar da aka yanke wa hukuncin kisa, ba dole ba ne su cancanci a yanke musu irin wannan hukunci.”

…Hukuncin kisan da aka yanke

Wata kotun birnin Riyadh na kasar Saudiyya ce ta yanke hukunci kisa ga wadansu mutum biyar daga cikin 11 da aka gurfanar a gabanta kan kisan dan jarida Jamal Khashoggi a karamin ofishin Jakadancin Saudiyya a Istanbul. Khashoggi, wanda aka kashe a bara, ya shahara wajen caccakar gwamnatin Saudiyya kuma wadansu jam’ian gwamnatin Saudiyya ne suka kashe shi a offishin jakadancin kasar da ke birnin Isntanbul na Turkiyya.

Kotun ta birnin Riyadh ta kuma yanke hukuncin daurin shekara 24 ga wadansu mutum uku, kuma ta sallami sauran. Kotun ta ce zaman shari’ar kisan dan jaridar ya gudana ne a gaban wakillan kungiyoyin kasashen duniya da kuma ’yan uwan dan jaridar.

Mai shigar da kara na gwamnatin Saudiyya ya bayyana cewa jami’an sun dauki wannan mataki na kashe Khashoggi ba tare da sanin gwamnatin Saudiyya ba, wanda hakan ya ja aka shigar da mutum 11 kara.

Yariman Saudiyya ya musanta hannu kafin a cikin watan Oktoba ya bayyana cewa, ya dauki cikakken alhaki a matsayinsa na jagora a Saudiyya musamman ganin cewa, wadansu mutane da ke yi wa gwamnatin kasar aiki ne suka aikata kisan.

Kisan gillar

Marigayi Jamal Khashoggi da ya shahara wajen sukar manufofin gwamnatin Saudiya, gabanin kisan gillar da aka yi masa a ranar 2 ga Oktoban bara aka gan Khashoggi mai shekara 59 kuma marubuci a jaridar Washington Post ta Amurka, yana shiga ofishin Jakadancin Saudiyya a Instanbul da nufin karbo wasu takardun shirye-sjiryen aurensa da budurwarsa, amma tun daga wancan lokaci ba sake jin duriyarsa ba. Daga bisani wasu bayanai sun ce, an yi gunduwa-gunduwa da namansa bayan mutum 15 sun kashe.

A baya dai Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) da  Majalisar Dinkin Duniya sun zargi Yarima Bn Salman da kitsa kisan dan jaridar, zargin da Yariman ya yi ta musantawa.