Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Duniya ta zuba wa ’yan sanda ido kan zabubbukan bana

A makalata ta makon jiya na bi sawun wasu daga cikin shirye-shiryen da Shugaban Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana wa duniya da hukumarsa ta sa gaba don tabbatar da nasarar zabubbukan bana da za ta fara gudanar na Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa nan da kwana 15, in Allah Ya kai mu. Bayan kawo jerin yadda zabubbukan za su kasance a waccan makala, na kawo yawan jam’iyyun da za su shiga zabubbukan da na takarar Shugabancin Kasa da na majalisun biyu, wato Majalisar Dattawa da ta Wakilai. Kai! Har ma da yawan wadanda za su kada kuri’a da suka kai mutum miliyan 80 da mutum dubu 4 da kuma 84,  wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu tun da aka fara mulkin dimokuradiyya a kasar nan yau kusan shekaru 20.

Na kuma fadi tabbacin da Shugaban Kasa Mahammadu Buhari da Shugaban Hukumar INEC daga lokaci zuwa lokaci su ke ta ba jam’iyyun adawa da kungiyoyin duniya da na cikin gida, musamman wadanda za su sa ido a kan zabe da shugabannin addinai da sauran ’yan kasa, cewa Hukamar INEC, za ta gudanar da zabubbukan cikin gaskiya da adalci, don samun sahihi kuma ingantaccen zabe a bana.

ADVERTISEMENT

A waccan makala na karkare da cewa hakkin gudanar da sahihi kuma ingantacen zabe ba kawai na kan Hukumar Zabe ita kadai  ba ce, a’a hakki ne da ya rataya a kan kowane dan kasa nagari. Dadin-dadawa, shi kansa magudin zabe, a kuma zauna lafiya, dama ce a inda ’yan siyasar suke da ita. Irin wannan rashin dama ce, kan sa wadansu su rika sace kayan zabe ko akwati dungurungum, ko kuma in duka sun faskara, sai su sa a ta da fitina ta yadda za a ce ba a yi zaben ba.

Mai karatu, yau makalar tawa kamar yadda ka iya karanta kanunta za ta mayar da hankali ne a kan irin rawar da ’yan sandan kasar nan ya kamata su taka don samun sahihi kuma ingantaccen zabe kamar yadda ake ta begen ganin an samu. Ina sane da cewa ba wai ’yan sanda kadai ke bayar da kariyar tsaro, a lokutan zabubbukan a kasar nan, akwai sauran jami’an tsaro kamar sojoji da Kwastam da Magireshin da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da sauransu. Amma zan yi batun ’yan sanda ne saboda hakkin samar da tsaro a lokacin zabubbukan kacokan ya rataya a kansu, tunda dai batu ake na mulkin farar hula ba yaki ba. Da kuma sanin cewa kashi 80 cikin 100, na jami’an tsaron da za su samar da tsaron a yayin zaben ’yan sanda ne, saura kashi 20 ne za su fito daga sauran bangarorin.

ADVERTISEMENT

Tunda ’yan sanda ke da hakkin samar da tsaro a lokacin zabe, kuma su ne mafi yawa a aikin, to, a takaice bari mu duba wasu daga cikin ayyukan da ya kamata ’yan sandan su gudanar a lokacin zabubbukan, bisa ga doka. A iyakacin fahimtata, ayyukan ’yan sandan a lokacin zaben ba su wuce biyar ba:-

1. Kare Turawan Zabe da kayayyakin zabe da harabar da ake yin zaben.

2. Su kuma kare lafiyar masu kada kuri’a da tabbatar da kowa ya kada kuri’arsa cikin walwala da kwanciyar hankali da annashuwa.

3. Na uku, su tabbatar da an yi kidaya cikin gaskiya da adalci kuma dukan wakilan jam’iyyu su amince da lissafin kuri’un da aka kada su kuma rattaba hannu a kai.

4. Su raka sakamakon zabe da sauran kayayyakin zabe zuwa cibiyar tattara kuri’u.

5, bisa ga umarnin Babban Baturen Zabe na mazabar da suke, su kama duk wanda Baturen Zaben ya ce su kama kan zargin ya aikata wani laifi a zaben.

Da wannan ke nan mai karatu za ka iya gane cewa kwadayi da son zuciya ke sa ’yan sanda wuce makadi da rawa a lokacin zabubbuka, har a rika samunsu cikin ayyukan magudin zabe irin na cika akwati da kuri’un da ba halattattu ba da kawar da kai a kan magudi ko wata fitina da ’yan daba ka iya tayarwa komai muninta, ha a wayi gari ’yan sandan su ce ba su kama kowa ba. Ina fata mai karatu ba zai ce ina tufka da warwara ba, kan tun farko na ce hakkin tabbatar da sahihi kuma ingantaccen zabe na kowa da kowa ne, yanzu kuma ina cewa na ’yan sanda ne. Abin da ya sa nake nanata batun ’yan sanda, don su ke da alhakin tsare doka da oda, kuma masu iya magana sun ce Sallah daga liman take baci.

Sanin kowa ne cewa a ranar 15 ga Janairu Shugaban Kasa ya nada Alhaji Adamu Abubakar Muhammad a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan kasar nan, bayan ajiye aikin da Alhaji Ibrahim Idris ya yi, kasancewar ya cika shekara 60 a duniya, kamar yadda doka ta tanada. Duk da sabon Sufeton Janar din ya karbi ragamar mulki a daidai lokacin da rigingimu irin fashi da makami da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sace-sacen shanu da kashe-kashen na ba gaira ba dalili da sunan rikicin kabilanci da addini da rikicin Fulani makiyaya da manoma, ga  na ’yan kungiyar namen kasar Biyafara, ga na Boko Haram da ya ki ci ya ki cinyewa, kuma ga hayaniya da tashe-tashen hankula irin na zabe, amma dai sabon Sufeto Janar din yana ta ba ’yan adawa da ita kanta Gwamnatin Tarayya da kasashen duniya da kungiyoyinsu tabbacin za su dage wajen ganin sun tabbatar da gaskiya da adalci ga kowa a zabubbukan.

Ita ma Hukumar Kula da Harkokin ’Yan sanda an ruwaito Kwamishinanta mai kula da shiyyar Kudu maso Kudu Mista Austin Braimoh lokacin da yake gana wa da Gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyesom Wike a garin Fatakwal kwanan baya yana cewa a wannan karon hukumarsu ta fitar da wasu sharudda 12, wadanda da su ’yan sandan za su yi aikin zabubbukan. Mista Braimoh ya fada wa Gwamnan cewa, hukumar ta kafa wani kwamiti da zai rika bin sawun ’yan sandan kan yadda suke gudanar da ayyukansu a lokutan zabubbukan, abubuwan da ya ce za su yi don bin sawun miyagun laifuffukan da ake zargin ’yan sandan na aikatawa a lokutan zabubbukan. Kodayake kasar nan na matukar bukatar addu’o’in a yi zabubbukan bana lami lafiya, amma kuma kuma kowa sai ya taka tasa rawar yadda ya kamata, musamman ’yan sanda da hakkin tabbatar da doka da oda ya rataya a wuyansu.