✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dutse mai aman wuta ya sa an kwashe dubban mutane a Philippines

An kwashe sama da mutum dubu 30 da ke zaune a Manila babban birnin kasar Philippines, a wurin da wani tsauni ke ta aman wuta…

An kwashe sama da mutum dubu 30 da ke zaune a Manila babban birnin kasar Philippines, a wurin da wani tsauni ke ta aman wuta da ruwan toka da kuma tururi – bayan da ya fara aman a ranar Lahadi.

Masana ilimin kimiyya a Cibiyar Binciken Karkashin Kasa ta Philippines sun kara gargadin kan fuskantar mummunan aman wuta cikin sa’o’i zuwa kwanaki.

Shugaban Cibiyar Mista Renato Solidum, ya ce, “Cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, Tsaunin Taal ya ci gaba da aman wuta inda muka yi ta ganin wasu al’amura biyu: Na farko shi ne tumbudin wuta; na biyu kuma garwayar ruwa da sauran abubuwan da ke fitowa a aman tanderun har yake cilla wa sama da tsawon kilomita biyu da kuma tokar da ke baduwa a yamma da kudu maso yammacin tsaunin na Taal.”

A kasar Ekwado kuma dutsen La Cumbre mai aman wuta ne ya yi bindiga. Wata kara mai karfin gaske tare da fashewa sun auku a dutsen na La Cumbre mai aman wuta da ke tsaunukan Galapagos na kasar ta Ekwado.

Sanarwar da mahukuntan waurin shakatawa na Galapagos suka fitar ta ce dusten na La Cumbre da ke Tsaunin Fernandina ya fara aman wuta. Sanarwar ta bayyana cewa dutsen ya fara aman wuta ce bayan shekara biyu – rabon da ya yi aman wutar. A shekarar 2018 ne dutsen ya yi aman wuta a karo na karshe.