✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ebola ba zai yi ritaya daga damben gargajiya ba

Fitatcen dan damben gargajiyar nan Muhammad Abdurrazak da aka fi sani da Ebola ya ce bai yi shirin yin ritaya daga wasan ba a yanzu.…

Fitatcen dan damben gargajiyar nan Muhammad Abdurrazak da aka fi sani da Ebola ya ce bai yi shirin yin ritaya daga wasan ba a yanzu.

Ebola wanda ke wakiltar bangaren Kudu da ke dambe da  hannun hagu ya ce kawo yanzu babu wani dan wasa da zai iya kare mutuncin Kudawa kamar yadda yake yi.

Dan wasan daga Jihar Kaduna ya ce kawo yanzu babu wani babban dan dambe da zai iya tare yaki da zarar ya tunkaro Kudawa.

Ya cew Shagonsa Taufik Dogon Ebola da Dan Alin Bata suna namijin kokari da sauran matasa, to amma wani damben ya fi karfinsu shi ya sa har yanzu yake yin wasa.

Akwai manyan ’yan dambe a bangaren Guramada da suke da jiki da karfi kamar su Dogo Mai Takwasara da Garkuwan Cindo da Dogon Kyallu da Habu na Dutsen Mari da  sauransu.

Haka ma a yankin Arewa akwai Ali Kanin Bello da Bahagon Shagon ’Yan sanda sai namijin gaske.

Ebola ne ya fara lashe mota a damben Kano da aka fara, kuma ya kai wasan daf-da-karshe a wasannin Kaduna a bana.

Ebola ya kara da Bahagon Shagon ’Yan Sanda a Dei-Dei inda wasan ya kai da takaddama, aka bai wa Bahago mota.

Sai dai sun kara haduwa a wasan karshe a damben Kaduna a Marabar Nyanya a Jihar Nasarawa, inda Ebola ya buge Bahagon Shagon ’Yan sandan.

Kawo yanzu kisa uku da uku ne a tsakanin Ebola da Ali Kanin Bello, yayin da Ebola ya yi nasarar buge Mai Takwasara 3-1.

Sai Sarkin Dambe Garkuwan Cindo da ya ci mota biyu a kan Ebola, amma bai yi kisa a wasan farko ba, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Sai a haduwa ta biyu ne Garkuwan Cindo ya buge Ebola.

Haka kuma Bahagon Mai Takwasara ya buge Ebola a bara a Abuja, koda yake Taufik ya daukar wa Ebola fansa inda ya buge Bahagon Mai Takwasara.

A bana Abdurrazak Ebola ya ce zai dauki fansa a kan Sarkin Dambe Garkuwan Cindo da Bahagon Mai Takwasara.

Ya kara da cewa zai kafa tarihin da bai yi shi a baya a harkar dambe zai kuma tsaya ya ci gaba da kare martabar Kudawa.

A harkar dambe Ebola ya samu alheri da dama yana kasuwanci da sauran hanyoyin da yake daukar nauyin ’yan uwa da abokan arziki sai dai bai yi aure ba kawo yanzu.