✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta zabi Buhari ya jagoranci yaki da COVID-19

Shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) sun zabi Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jagoranci yaki da cutar coronavirus…

Shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) sun zabi Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jagoranci yaki da cutar coronavirus a fadin yankin.

Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara ta Fuskar Yada Labarai Femi Adeshina ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da hakan a karshen wani taron gaggawa da shugabannin suka gudanar.

NAN ya ruwaito cewa taron, wanda shugabannin suka kirawo, ya mayar da hankali ne kacokan a kan annobar COVID-19 wacce take ci gaba da daukar rayukan jama’a a fadin duniya.

Da yake bude taron, shugaban ECOWAS, wanda kuma shi ne shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Issoufou, ya ja hankalin sauran takwarorin aikinsa a kan irin illar da wannan annoba take yi a kan bil-Adama da kuma tattatin arzikin kasashen da ke wannan kungiya.

Haka kuma Mahamadou Issoufou ya jinjina wa Bankin Duniya da kuma Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) a kan irin rawar da suke takawa wajen dakile yaduwar cutar a nahiyar Afirka, sannan ya nemi su ci gaba da ba da gudunmawa don ceton rayukan al’umma.

Kimanin shugabannin kasa 13 ne ciki har da Shugaba Buhari suka halarci wannan taro.