✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC: Kwamitin binciken Magu ya kai wa Buhari rahoto

Kwamitin Mai Shari'a Ayo Salami ya kai wa Buhari akwatunan bayanai kan zargin Magu

Kwamitin Shari’a mai binciken zargin da ake wa tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, ya kai wa Shugaba Buhari rahotonsa.

‘Yan kwamitin na Mai Shari’a, Ayo Salami sun isa Fadar Shugaban Kasa dauke da akwati hudu na hujjoji da zai mika wa Shugaba Buhari kan aikin da ya gudanar kan zargin Magu.

A watan Yuni Shugaba Buhari ya kafa kwamitin domin gano gaskiyar zarge-zargen da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi wadanda suka kai ga dakatar da Magu daga mukaminsa.

Malami na zargin Magu da laifuka 22 na karkatar da kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati, rashin biyayya ga Ministan Shari’a da fifita wasu jami’an EFCC a kan wasu da dai sauransu.

Bayan kai ruwa rana da tambayoyi da kwamitin ya yi wa manyan shugabannin EFCC, an nada Babban Darektan Gudanarwanta, Mohammed Umar, a matsayin mukaddashin shugaba zuwa lokacin da kwamitin zai kammala aikinsa.

Daga baya an kara wa’adin aikin kwamitin daga kwana 45 bayan ya bukaci karin lokaci.

Ana gabatar rahoton binciken ne a ranar da Shugaban EFCC na farko, Malam Nuhu Ribadu ke cika shekara 60 da haihuwa.