✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta bankado cibiyar koyar da ‘yan dafara a yanar gizo

Jami’an Hukumar da ke yaki da rashawa a Najeriya EFCC da ke aiki a babban ofishin hukumar na Legas sun yi nasar bankado wata cibiyar…

Jami’an Hukumar da ke yaki da rashawa a Najeriya EFCC da ke aiki a babban ofishin hukumar na Legas sun yi nasar bankado wata cibiyar koyo da koyar da masu danfara ta yanar gizo wadanda aka fi sani da ‘yan Yahoo-Yahoo ke amfani da ita wajen samun horon danfara a yanar gizo.

Jami’an sun kame mai koyar da dabarun danfarar matashi mai kimanin shekaru 22 mai suna Frank Chinedu tare da daliban cibiyar su takwas, inda aka same su da na’ura mai qwaqalwa 9,  da wayar salula 16 da tarin Latin waya da sauran su.

A wata sanarwa da hukumar ta EFCC t ayi a kafar sada zumunta ta yanar gizo ta shaida cewa, a ranar 22 ga watan nan ne ta kame wadanda ake zargin biyo bayan bayanan asiri da ta tattaro akan su za kuma a gurfanar da su a gaban kuliya nan bada jimawa ba.