✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama ’yan damfarar yahu-yahu 94 a gidan rawa a Osogbo

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta kama matasa 94 ‘yan damfarar yahu-yahu da kananan motocin alfarma 19 da na’urorin…

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta kama matasa 94 ‘yan damfarar yahu-yahu da kananan motocin alfarma 19 da na’urorin kwamfuta mai kwakwalwa laptop da wayoyin salula masu yawa a tare dasu.

An kama su ne a yau Litinin da safe a wani gidan rawa mai suna ‘Club Secret Underground ‘da ke garin Osogbo Hedkwatar Jihar Osun.

Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da Kakakin (EFCC) shiyyar Ibadan Mista Jide Jegede, ya rabawa ‘yan jarida.

‘Yan yahu-yahu da aka kama

Ya ce, dirar mikiyar da jami’an EFCC suka yi a gidan rawar ya biyo bayan samun labarin sirri ne da ya kaisu ga samun nasarar kama wadannan matasa.

Ya ce, yanzu haka sun fara binciken lamarin. Kuma da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wadannan matasa gaban kotu ne domin yanke musu hukuncin daidai da irin laifin da suka aikata.

Wayoyin salula da aka kama