✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kwato fiye da Naira Miliyan 55 a Gombe

Hukumar EFCC a Shiyyar Arewa maso Gabas da ke da ofishi a Gombe ta ce a cikin wata hudu na farkon bana, ta kwato kimanin…

Hukumar EFCC a Shiyyar Arewa maso Gabas da ke da ofishi a Gombe ta ce a cikin wata hudu na farkon bana, ta kwato kimanin Naira miliyan 55 da dubu 627 da 340 da kwabo 18 daga hannun mutane daban-daban da ake zargin sun yi amundahanarsu.

Shugaban Hukumar a Shiyyar, Mataimamin Babban Sufurtandant mai kula da bangaren bincike na hukumar, Michael T. Wetkas ya bayyana haka a Gombe lokacin wani taron manema labarai da suka kira.

Ya ce aikinsu a wannan shiyyar ya karu domin sun samu korafe-korafe 81 kuma sama da 70 sun zo ne daga sauran jihohin shiyyar, yayin da sauran kuma suka same su daga Gombe.

Michael T. Wetkas ya kara da cewa sun tura wadanda ake zargi da laifuffuka 37 gidan yari, 41 suna kotu daga watan Janairu zuwa Afrilun bana.

A cewarsa kadarori da suka mika wa Gwamnatin Tarayya sun kai na Naira miliyan 18 da dubu 800, sannan akwai wata kara a gaban Mai shari’a Bilkisu Bello ta Babbar Kotun Tarayya da ke Yola, inda ta daure wadansu mutane ta kwato motoci biyu kirar Fijo da Honda Cibic.

Daga nan sai ya ce lokacin zaben da ya wuce Hukumar EFCC ta kama mutum takwas da laifin sayen kuri’u cikinsu har da Shugaban wata karamar hukuma a yankin.