✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Effiong ne kan gaba a cin kwallo a Firimiyar Najeriya

Dan wasan Akwa United, Ndifreke Effiong shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Firimiyar Najeriya. A karshen mako ne aka yi fafatawar mako…

Dan wasan Akwa United, Ndifreke Effiong shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Firimiyar Najeriya. A karshen mako ne aka yi fafatawar mako na 21, kuma kawo yanzu Effiong yana da kwallo 10 a raga. Bictor Mbaoma na Enyimba International ya ci tara, shi ne na biyu  a cin kwallo a gasar.

Sashin Hausa na BBC ya rubuta a shafinsa na Intanet cewa, ’Yan wasa uku ne ke kan-kan-kan da kowanensu ya zura kwallo takwas a raga. ’Yan wasan sun hada da Tasi’u Lawan na Katsina United da Ibrahim Mustapha na Plateau United da Israel Abia na Rangers International.

Bayan buga wasannin mako na 21, Plateau United tana a mataki na daya da maki 37, sai Ribers United ta biyu da maki 36, sai Lobi Stars ta uku wadda ita ma makinta 36.

A wani labarin, kulob din Jigawa Golden Stars ya doke Wikki Tourist da ci 2-1 a wasan mako na 21 a ranar Lahadi a Kano. Minti biyu da fara wasa ne Wikki ta fara cin kwallo ta hannun Promise Damala, kuma haka aka je hutun rabin lokaci.

Sai dai bayan sun koma zagaye na biyu ne Jigawa ta farke ta hannun Ibrahim Saleh, sannan Abdullahi Lala ya kara ta biyu.Kano Pillars ma ta yi rashin nasara ne da ci 2-1 a gidan Ribers United. Ribers ce ta fara cin kwallo ta hannun Konan Ruffin N’Gouan a bugun fenariti, sannan Cletus Emotan ya ci ta biyu saura minti biyu a tashi wasa.

Kyaftin din Kano Pillars, Rabi’u Ali ne ya rage musu zafi inda ya ci kwallo daya dab da alkalin wasa zai hura tashi.

Plateau United wadda ke jagorantar teburin gasar ta tashi 0-0 a gidan Lobi wadda take ta biyu a teburin.