✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufa’i ne daidai da Kaduna – Sarkin Samari

Sarkin Samarin Jama’a Alhaji Mudi Shfi’u Tahir ya bayyana Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i a matsayin Gwamnan da ya dace da Jihar Kaduna…

Sarkin Samarin Jama’a Alhaji Mudi Shfi’u Tahir ya bayyana Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i a matsayin Gwamnan da ya dace da Jihar Kaduna domin salon tafiyarsa ce kadai za ta iya kawar da siyasar kabilanci da ta addini da ta mamaye siyasar jihar musamman a yankin Kudancin jihar.

Sarkin Samarin Masarautar Jama’are ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da Aminiya a garin Kafanchan.

Sarkin Samarin, ya ce maimakon fassarar da wadansu ke yi wa Gwamnan kan zabin Mataimakiya Musulma a matsayin abin da zai haifar da siyasar addini tsantsa, kamata ya yi su fahimci hakan a matsayin fahimtar da wadanda ba su sani ba cewa yin hakan ne kadai matakin da ya dace wanda zai nuna wa duniya cewa yankin Kudancin Kaduna yanki ne na Musulmi da Kiristoci gaba daya ba wai na wani addini ko wata kabila guda daya ba da yawancin wadanda su ka jahilci yankin suke tunani ko kuma kallo daga nesa.

“Akwai jama’a da dama da idan ka ce musu Kudancin Zariya ko Kudancin Kaduna tunaninsu kawai shi ne kamar wani yanki ne na wasu kabilu mabiya addinin Kirista zalla, alhali ba haka abin yake ba. Ina tunanin domin sauya wa sauran jama’a irin wannan tunani ne ya sa Gwamna Nasir El-Rufa’i ya dauko Musulma ’yar asalin daga yankin wacce take ba Bahaushiya ba, don a fahimci cewa shi ma kamar sauran yankuna ne, ya kunshi Musulmi ne da Kiristoci,” inji shi.

Sarkin Samarin ya kuma bayyana cewa idan har Gwamnan ya yi nasara to ya bude wa wadanda za su zo baya ido ne cewa wadansu marasa son ci gaban jihar ne kawai suke fakewa da yankin Kudancin Jihar suke shuka maganar addini don cimma burin siyasa kawai.

“Nasararsa za ta nuna cewa gobe wadansu ba za su fake tare da zuga wadansu a kan maganar addini da siyasa a jihar ko yankin ba. Kudancin Kaduna sun fitar da fitattun mutane da suka bayar da gagarumar gudunamwa da ci gaba ba Jihar Kaduna ba kawai har da kasa baki daya. Daga cikinsu akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, marigayi Wazirin Jama’a Alhaji Aliyu Muhammad,”  inji shi.