✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufa’i ya cika alkawari ya sa dansa a makarantar gwamnati

A ranar Litinin da gabata ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya cika alkawarin da ya dauka shekarun baya cewa zai sa dansa…

A ranar Litinin da gabata ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya cika alkawarin da ya dauka shekarun baya cewa zai sa dansa Abubakar Saddikue El-Rufa’i a makarantar gwamnati.

Gwamnan tare da mahaifiyar dan, Ummi El-Rufa’i ne suka kai Abubakar dan shekara shida makarantar Kaduna Capital School da ke a Malali Kaduna inda aka yi masa rajista.

Shugaban Makarantar Ibrahim Yunusa ya tabbatar wa Aminiya cewa an yi wa yaron rajista a makarantar kamar yadda ake yi wa sauran dalibai.

“Eh a ranar Litinin da safe Gwamna El-Rufa’i da matarsa sun zo makarantar nan inda suka yi wa dansu Abubakar Siddikue El-Rufai rajista a aji daya na firamare. Na kuma yi murna da karbar dan nasa domin hakan zai taimaka wajen inganta makarantun gwamnati. Gwamnan ya kuma bayyana min cewa ya zo ne a matsayina na uba kamar kowa sannan ya cika alkawarinsa  ga jama’a,” inji shi. Shugaban makarantar ya ja hankalin sauran masu rike da mukaman gwamnati su yi koyi da Gwamnan domin yin hakan ne zai taimaka wajen maido da martabar makarantun gwamnati.

Da yake magana a ranarsa ta farko a aji, Abubakar Siddikue ya ce duk da cewa zai yi kewar barin makarantarsa ta da, da abokan karatunsa da malamansa, ya ce ya yi hakan ne domin ya taimaki mahaifinsa ya cika alkawarin da ya yi wa mutane.

An dai kafa makarantar Kaduna Capital School ce a 1957 kuma makarantar gwamnati ce.