✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Zakzaky ya ce yana cikin koshin lafiya

Shugaban kungiyar harkar musulunci ta IMN wacce ake kira Shi’a, Shaikh Ibrahim El-Zakzaky ya fadawa manema labarai cewa yana cikin koshin lafiya.   A karshen…

Shugaban kungiyar harkar musulunci ta IMN wacce ake kira Shi’a, Shaikh Ibrahim El-Zakzaky ya fadawa manema labarai cewa yana cikin koshin lafiya.
 
A karshen makon da ya gabata an yi ta yada jita-jitar mutuwarsa a kurkukun hukumar tsaro ta SS inda ake tsare da shi shekaru biyu da suka gabata.
 
Sakonnin wayar salula da sakonnin kafar sada zumunta ta whatsApp sun yi ta bazuwa kamar wutar daji inda aka rika yada cewa El-Zakzaky ya mutu a kurkukun da ake tsare da shi sakamakon raunin da ya ji na harbin bindiga yayin da aka yi kokarin kama shi.