✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: Buratai ya yi fatali da rahoton CNN

Rundunar Soji Kasa ta ce cikin kwarewa dakarunta suka tunkari masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki.

Rundunar Sojin Najeriya ta yi watsi ta rahoton kafar watsa labaran Amurka, CNN, kan zargin sojoji da harbin masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Jihar Legas.

CNN na zargin sojojin sun harba wa masu zanga-zangar harsasai masu rai, amma rundunar ta ce dakarunta sun gudanar da aikinsu cikin kwarewa da “kiyaye dokokin aiki”.

Rahoton kafar ya ce ya gano wani Victor Sunda Ibanga da ya mutu a daren da sojojin suka yi harbe-harben, kuma gwajin kwanson harsasan da aka harba wa masu zanga-zangar ya nuna masu rai ne.

Ta ce kwararru biyu a kan makamai sun tabbatar mata cewa kwanson harsasai masu rai ne, sannan wani tsohon sojan Najeriya da wani mai aiki a yanzu sun ce siffar kwanson harsasan “ta yi daidai da na sojojin”.

Kafar ta ce ta yi aiki tare da Cibin Binciken Kwakwaf ta Balkan kuma sun “gano yawancin albarusan da aka harba a Lekki an samo su ne daga kasar Serbia.

“Takardun bayanan ciniki da CNN ta samu sun nuna Najeriya ta sayo makaman ne daga Serbia kusan duk shekara daga 2005 zuwa 2016”.

Cikin kwarewa muke aiki —Buratai

A martaninsa ga rahoton, Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce rundunar ta san aikinta kuma ba za ta taba saba dokokin aikinta ba.

Da yake karbar bakuncin Kwamitin Rundunar Sojin Kasa na Majalisar Wakilai a Hedikwatar Tsaro, Buratai ya yi watsi da rahoton na CNN.

“Ina tabbatar muku cewa Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya kwararriya ce kuma muna bin dokokin aikinmu.

“Yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, muna bin dokokin aikinmu da kuma Tsarin Mulkin Najeriya sau da kafa”.

Buratai ya kara da cewa “sojoji na maganin” ’yan bindiga a kan babbar hanyar Abuja-Kaduna.

Tun da farko, Kwamitin na Hon. Abdulrasaq Namdas, ya ce ya ziyarci Hedikwatar Rundunar ce domin bayyana abubuwan da ya gano a lokacin aikinsu na sa ido a rundunonin soji a fadin Najeriya.

Sai dai Namdas bai kai ga bayyana wa Buratai abubuwan da kwamitin nasa ya gano ba sai da aka sallami ’yan jarida.