✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: El-rufa’i ya kara fadada dokar hana fita a Kaduna

Ya kuma ce dokar zaman gidan ta gama-gari za ta fara aiki nan take.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 da za ta game jihar baki daya sabanin sanarwar farko da ta takaita a wasu kananan hukumomin jihar biyu da suka hada da Chikun da Kaduna ta Kudu, inda a yanzu dokar ta game baki daya kananan hukumomi 23 da ke jihar.

Jawabin ya fito ta bakin Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin gida, Samuel Aruwan a daren Asabar, ya kuma ce dokar zaman gidan ta gama-gari za ta fara aiki nan take.

Gwamnatin jihar ta ce ta dauki wannan matakin saboda da kare lafiya da dukiyoyin al’umma da dakile shirin bata-gari na satar kayayyakin gwamnati.

Kwamishinan ya bukaci jama’ar jihar Kaduna da su zama ‘yan kasa jakadu nagari, kuma su bawa gwamnatin jihar dukkan hadin kai da goyan baya su kuma kiyaye doka da oda da bin umarnin gwamnati kamar yadda aka bukata.