✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

#EndSARS: Farashin shinkafa ’yar waje ya fadi warwas

Farashin shinkafa ’yar waje ya karye bayan ’yan sumoga sun samu shigo da ita a lokacin rikici

Farashin shinkafa ’yar waje ya karye a Jihar Ogun bayan ’yan sumoga sun samu sake sakamakon rikicin da ya biyo bayan zangar-zangar #EndSARS inda suka ba da himma wajen shigo da ita daga iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin da ke daura da jihar.

Wasu mazauna sun shaida wa Aminiya cewa tun ranar Talatar makon jiya masu fasakwauri suka samu dama bayan rikicin ya kaure a jihohin Legas da Ogun, wanda ya sa jami’an tsaro janyewa daga shingayensu a kan iyakokin kasashen biyu a jihar Ogun.

Hakan, a cewarsu, ya bai wa ’yan sumoga damar shigo da shinkafar babu kakkautawa, har sai da farashin buhunta ya ragu da N8,000.

Malam Manniru Muhammed dan kasuwa ne da ke sayar da kayan abinci a kasuwar Lafenwa da ke Abeokuta.

Ya shaida wa Aminiya cewa zuwa yanzu ana sayar da bubun shinkafa ’yar waje a kan N17,000 zuwa N18,000 sabanin N25,000 zuwa N26,000 da ake sayarwa a baya.

“Saukin da shinkafar ta yi a Jihar Ogun ba yana nufin an bude boda ba ne.

“Ka san yanzu babu ma’aikatan da ke tatsar kudi daga masu fasakwaurin; mafi yawansu sun janye a sakamakon rikicin da ya biyo bayan zanga-zanga.

“Don haka ’yan sumoga suka samu suna shigo da shinkafar cikin sauki, amma ni ban sami ikon saya ba saboda kasuwar tamu muna cikin dardar wasu bata-gari na neman tayar da rikici.

“Yanzu haka ma zan rufe rumfata in tafi gida saboda gudun kar rikicin ya rutsa da ni”, inji shi.

Wakilin Aminiya ya gane wa idon sa yadda masu ’yan sumoga ke fasakwaurin shinkafa a kan babura da motoci zuwa Abeokuta ta hanyar Ayetoro mai iyaka da Jamhuriyar Benin.

Jami’an kwastam na fuskantar barazana

Kakakin Hukumar Kwastam ta Kasa a Jihar Ogun, Hammed Bokoye Oloyede ya shaida wa Aminiya cewa ’yan sumoga na amfani da rikicin zanga-zangar #EndSARS suna fasakwauri.

Ya ce jami’ansu na yin taka tsantsan ne domin guje wa tayar da zaune tsaye.

“Akwai wurare da dama da muka janye jami’anmu muka hade su da na wani wajen domin kara masu karfi duba da harin da ake kai musu, kuma yanzu akwai wurare da dama da aka turo sojoji domin su karfafi jami’anmu”, inji shi.

Ya ce ko a ranar Talata 20 ga watan Oktoba bata-gari a cikin masu zanga-zangar #EndSARS sun kai farmaka akan jami’an kwastam da ke aiki a yankin Oke Ore a Karamar Hukumar Yewa ta Kudu.

“Bata-garin dauke da muggan makamai sun hallaka jami’in kwastam mai suna Solomon Alagye sun kuma raunata wani da a yanzu yake samun kulawa a Asibitin Aojoji da ke Owode.

“An kira sojoji domin kai musu dauki amma shingayen da masu zanga-zangar suka sanya ne suka hana a isa wurin a kan lokaci”, inji shi.

Sakamakon zanga-zangar #EndSARS, muhinmman wurare da dama da a baya jami’an tsaro kan tsaya domin tabbatar da doka da oda a Jihar Ogun sun kasance matattaran miyagu da ke karbar kudi a hannaun masu wucewa da kaya a cikin motoci ko babura.